Connect with us

RIGAR 'YANCI

Mu Na Samun Nasarori A Fannin Kasuwancin Dabbobi A Legas – Bala Katato

Published

on

Daya daga cikin shuwagaban ni masu kulawa da kasuwancin dabbobi a legas mai Suna (MD) Alhaji Bala Katato na bangaren kamfanin Afirel sistin sistin 16-16 dake kasuwar sayar da dabbobi abbatuwa okoba Agege a cikin garin legas ya bayyana cewar shida sauran shuwagaban nin kasuwar sayar da dobbobi na wannan kasuwa suna cigaba da samun nasarori daban daban a wajan kasuwanci dabbobi bakidaya MD Bala Katako yayi wan nan tsokaci ne a legas a ofis dinsadake Afirel sistin sistin a lokacin da yake zan tawa da wadansu wakilan kafofin yada labarai na kasa domin shai da masu wannan alamari

Ya cigaba da cewa kadan daga cikin nasarorin da suka samu sun hada da zaman lafiya ga alumma tareda gudanar da kasuwancin dabbobi a cikin tsari da kwanciyar han kali da sauran makaman tansu ya kara dacewa akan haka nema a matsayinsa na shugaban wannan ban gare na kulawa da kasuwancin dabbobi yake kara isar da godiyarsa ga Allah madau kakin sarki da ya sanya suke zaune lafiya da junansu da sauran alumma da kabilun cikinsu bakidaya kuma ya cigaba da cewa zai cigaba da tsayawa tsayin daka tareda jajir cewa na kare hakkokin alummar wannan kasuwa tareda dukiyoyin su bakidaya

Sannan ya cigaba da isar da sakonsa ga alummar kasuwar dasu kara kai mi awajan neman zaman lafiya da junansu tareda hadin kai domin cigaba da samun nasarori irin wadan nan na zaman lafiya tare da sauran alamuran da suka shafi halim zaman takewar junansu a legas da kuma kewayen ta bakidaya sannan yacigaba da isar da sakonsa ga gwamnatin jihar legas ako karinta.

Na kare lafiya alummar jihar awajan kaucema kamuwa da annobar cutar kurona bakidaya ya cigada da cewar wannan cuta cutace data zagaye duniya ba gida Nijeriya ba kadai yace akan haka yake ummar alumma Nijeriya da na sauran kasa shen duniya musamman kasashenda musulmi suke da sauran kiris toci da su cigaba da gudanar da addu OI na musamman domin Allah ya tau saya mana ya kawar ma da alumma wannan cuta bakidaya injishi da fatan Allah Ubanji zai karbi rokon alumma bakidaya

Katako yacigaba da shawartar alummar Nijeriya dasu cigaba da yima shuwagaban nin kasar nan adduOI na musamman akokarinsu na jagorancin Jamaa a mai makon miya gun kalamai da su ke yi ya kara da cewar idan al’umma na yi wa shuwagabani addu’o’i na musamman injishi koda shuwagaban nin marasa adalci ne sai kaga Allah ya gyarasu sun dawo masu adalci acewarsa da fatan alummar Nijeriya zasu karbi wadan nań shawar wari nashi bakidaya

Sannan kuma ya cigaba da ummurtar alummar arewacin Nijeriya mazauna legas dasu cigaba da zaman lafiya da sauran kabilu mazauna cikin garin legas dake wayen ta bakidaya domin kaucema faruwar fada ce fadace awadansu lokuta yakara da cewar haka suma sara kuna shuwagabannin alummar hausawa mazauna legas dasu cigaba da taka rawa ta musamman a wajan ilmantar da mabiyansu a wajan nuna mäsu mahimmancin zaman lafiya da sauran abubuwan da zasu inganta harkokin rayuwarsu bakidaya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: