Connect with us

RIGAR 'YANCI

Mu Na Samun Nasarorin Zaman Lafiya A Legas Da Kewaye – Mahammadu Inuwa

Published

on

  • Shugaban Al’ummar Ya Nemi Hausawa Su Bi Umarnin Gwamnati Kan Korona

 

daya daga cikin shuwagabannin al’ummar Hausawa mazauna Jihar Legas mai suna Alhaji Mahammadu Inuwa wanda ya ke zaune a unguwar Marinbic N.R.C Reluwe Kwatas a Apapa da ke cikin garin Legas ya bayyana cewar al’ummar Hausawa mazauna jihar su na cigaba da samun nasarorin zaman lafiya tare da sauran kabilu abokan zamansu a Legas bakidaya.

Alhaji Inuwa ya yi wannan furuci ne a ofishinsa da ke unguwar Marinbic N.R.C din lokacin da ya ke karbar bakuncin wadansu Yarabawa da su ka fito daga unguwanni daban-daban da ke cikin Apapa da kewayenta, adanda su ka kawo masa ziyarar ban girma tare da neman karin jaddada dankon zumunci a tsakaninsu, domin su cigaba da zaman lafiya bakidaya.

Da ya ke gudanar da jawabinsa na jin dadi tare da nuna farin cikinsa a game da wannan ziyara da su ka kawo ma sa, shugaban, Alhaji Inuwa N.R.C, bayan ya kammala yi mu su maraba da lale, ya cigaba da shawartar su da su cigaba da hada kawunan junansu tare da gudanar da irin wannan ziyarar, domin kara cigaba da samun zaman lafiya a tsakanin al’ummar Hausawa mazauna Legas da sauran kabilun da su ke zaune a jihar.

Ya cigaba da shawartar su da cigaba da bin umarnin shuwagabanninsu tare da bin dokokin Gwamnatin Jihar Legas, musamman dokokin da ta shimfida domin kauce wa kamuwa da wannan annoba ta cutar Korona da sauran dokokin gwamnatin jihar da kasa bakidaya, sannan ya cigaba da yaba wa sarkin al’ummar Hausawa mazauna unguwar, Alhaji Almustapha, a kokarinsa na hada kawunan al’ummar Hausawa da ba su shawarwarin da za su amfane su.

Sannan kuma ya cigaba da kara rokon Gwamnatin Jihar Legas da ta kara duba yiwuwar bude cibiyoyin gudanar da addinai daban-daban da ke fadin jihar ta Legas.

Ya kara da cewar duk da dai a na samun rahotanni su na nuna cewar kullum a na samun hauhawar wadanda su ke kamuwa da cutar ta kurona anan cikin Jihar Legas, ya ke ganin cewar yakamata Gwamnatin jihar ta legas ta bude da kunan gudanar da addinai masallatai da sauran coci-coci domin alumma su cigaba da gudanar da Ibadunsu tare da gudanar da addu’o’i na musamman domin Allah madaukakin sarki ya kawar mana da wannan annoba ta cutar Korona da sauran cututtuka bakidaya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: