Bishiya na zama garkuwa ta zaman lafiya ga mazauna birni sakamakon alfanun da ke tattare da ita ga rayuwar dan’adam, domin tana samar da abuwa da dama ga suka ta’allaka da walwala da jin dadin rayuwa a kowane muhalli, amma kash gwamnatocin jihohi sun yi kunnnen uwar shegu da muhimmanci bishiya ta hanyar sare su domin bada umarni ga masu hali su yi gine-gine don kasuwanci wanda hakan na da illa sossai ga bangaren lafiya da walwalar jama’a mazauna birane. A kullum yakamata hukumomi su san da cewa ci gaban birane ba tare da la’akari da me zai je ya dawo sakamakon ayyukan ci gaba, ba dai dai ba ne domin shi ne abin da Bahaushe ke cewa gyarar gangar Auzinawa, musamman ta bangaren lafiya da jindadin jama’a da ke takure a cikin birane.
Kariya Daga Dumamar Birane: Sakamakon sare bishiya da ke zama garkuwa ga muhalli ta hanyar kare shi daga tsananin zafi wanda ke da illa ga lafiyar jama’a mazauna manyan birane, misali jihar Kano na da tasawirar ci gabanta na shekara ashirin amma yanzu tana da sama da shekara hamsin da kafuwa maimakon samun kari a kan abin da aka tarar na shuke-shuke a cikin birnin tun a wancan shekaru da suka shude , gwamnatocin ba su mai da hankali wajen karin ba sai dai sare ‘yan kadan da suka rage suke yi sakamakon bukatu da ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa suke da sun a mallakar filaye domin kasuwanci. Maimakon bunkasu wasu guraren da ke wajen kwaryar biranensu domin fadada kowa ya nace sai dai ya mallaki abin da ya zama na jama’a baki daya saboda nuna isa ko karfin mulkin wanda hakan ba zai Haifar mana da mai ido ba.
Kariya Daga Cututtuka Masu alaka da Zafi: Sakamakon sare bishiya dake bada kariya ga dan’adam kare jikinsa daga zafi da ke samuwa sakamakon hayaki daga Babura, motoci da kuma injina, wannan nada matukar illa ga lafiyar mazauna birane wanda hakan na zama sanadiyyar samun cutuuttuka kamarsu asma, ciwon ido, cutar da ta shafi fatar jiki da sauransu, domin ita bishiya tana tattatre duk wata kura da hayaki ta kuma tattarasu ta watsa sama domin kariya ga muhalli, yakamata gwamantoci su daina mallakawa jama’a gurare da aka samar da su domin jama’a.
Kariya Ga Itatuwan Gargajiya: Wata babba matsala da ke faruwa sakamakon sare bishiya a manyan birane da gandun daji shi ne rasa tsufaffin bishiyayo da ka zama abin tarihi ga yara masu tasowa , musamman a wannan zamani na neman ilimin kimiyya, tarihi da al’adu da masana ke amfani da fasahar sadarwa wajen binciko abubuwan tarihi da ala’adu na gurare daban-daban a fadin duniya ba tare da an je ba, kuma hakan na bai wa kasa samun kudaden shiga sakamakon zuwan baki don duba tsufaffin kayan al’adun gargajiya musamman a kasashenmu masu tasowa sakamakon sare tsofaffin bishiyoyi masu tarihin gaske da kuma amfaninsu ga dan’adam da muhalli domin da yawansu kan samar da magunguna da kuma kariya ga muhalli ta hanyar rage gudun ruwa da zuke gurba tacciya iske da ka iya zama barazana ga rayuwa dan’adam da dabbobin da tattare a cikin biranenmu sakamakon rashin wadannan tsoffin iri na gargajiya. Misali akwai itatuwa da dama da yanzu idan ba gidajen manyan sarakunan gargajiya ka shiga ba ba za ka taba samunsu ba wadanda hakan barazana ce ga masana tarihi da al’adunmu na gargajiya, kasashen da suka ci gaba na mayar da tsofaffin bishiya gurin adana tarihi domin yara masu tasowa amma a Nijeriya kullum jama’a kokari suke su samu dama su sare abin da yayi saura na wadannan bishiyoyin wanda hakan ya zama abin kunya ne a gare mu daliban ilimi domin hakan na jawo koma baya ga cikin gaban wasu fannonin kamar su bangaren ilimin kimiyyar muhalli, da na tarihi da sauran fannoni da ke da alaka da ci gaban dan’adam.
Kariya Daga Zaizayar Kasa:
Bishiya na daya daga cikin hanyoyi masu sauki wajen kare zaizayar kasa a saukake kamar yadda yawancin manoma suka sani ruwa yana kwashe albarkar gona musamman taki da ke zama abinci ga shuka musamman a guraren da suke da gangara ko kuma wajen kasa mai laushi wanda hakan yakan janyo asarar amfanin gona, dakuma mayarda kasar noma takoma saimo, bishiya na kare shuka daga karyewa a sakamakon iska mai karfi.
Ma’ajiya Ruwa Da Iska: Gandun daji wata mattatara ce ta lafiyayyar iska da dan’adam ke shaka domin ya rayu kowa na sane da cewa duk gurin da ke da shukoki masu yawa ba ya kasancewa cikin yanayin zafi domin akwai iska mai sanyi sakamakon numfashin da bishiya ke fitarwa mai sanyi ce, wannnan iska da take fitowa daga tsirrai ita ce mutane ke bukata domin samun ingantacciya rayuwa, saboda haka ne idan za mu lura a kasashen da suka ci gaba ba sa wasa da shuke-shuke domin samun ingantacciyar rayuwa.
Kariya Daga Kwararowa Hamada:
Hakika sare itace babbar illa ce da ke haifar da masifu iri dadan-daban ga rayuwa bil’adama domin hakan na jefa muhalli cikin halin ni ‘yasu kamar yadda muke gani a kasashe kamarsu Nijar da Chadi, Libya da sauran kasashe na Arewacin Africa wanda hakan nada tasiri sosai wajen tattalin arzikin jama’arsu, kasar noma takan zamo ta kare sakamkon rashin samun rowan sama sakamakon rashin bishiya dake zama daya daga cikin hanyoyi dake samarda ruwan sama ta hanyar komawa dashi sararin samaniya sakamakon numfashin da tsirrai keyi. Yawanci guraren da babu bishiya na zama da iska mai zafi sakamakon rashin ni’ima da rowan sama ke samarwa kasa , saboda haka yazama wajibi idan hard an Adam nason jin dadi rayuwa to juri shuka bishiya kamar yadda yake sare ta.
Ya zama dole gare mu da mu kula da muhallinmu ta hanyar canja halayanmu a kan dazukanmu domin kare su shi ne hanya kadai da duniya za ta zauna lafiya.