Yusuf Kabir" />

Muhammad Danjuma Katsina Gwarzon Dan Jarida A 2020.

A wancan satin da ya wuce, mun nausa Duniyar Fina-finai a yayin da muka yi jinjina ga jarumi Lawan Ahamad (Izzar So) a yanzu kuma mun nausa Duniyar aikin Jarida domin fashin baki dangane da gwarzon dan Jarida Mal. Muhammad Danjuma Katsina.
Shi gogaggen dan Jarida ne da ya san aikinsa tattare da bayyana gaskiya a yayin aikin,hakan ya sa ya sha tsallake hadarurruka masu tarin yawa, a shekarar 2017 ma sai da ya shiga gidan jarum saboda ya yi rubutu a kan wani dan Majalissa a Jihar Katsina.
Takaitaccen Tarihin Marubucin!
Shi ne Muhammad Danjuma Katsina daya daga cikin shaharrun Katsinawan da sunan su ya yi tambari a Duniya. Ya kasance a kowane lokaci cikin fafutikar tallafawa al’ummomi ba tattare da lura da bambancin addini, kabila, yare ko launin fata ba.Hamshakin dan Jarida ne da rahotanninsa suka zamanto dalilin dakatar da aiwatar da rashin gaskiya,ko kuma suka zamanto dalilin wankewar wadanda ake zargi da laifi daga zargi. Bugu da kari ya zamanto gata ga raunanan mutane wajen isar da bukatunsu ga Hukumomin a matakin kasa ko kuma Jiha.
Mukaman Da Ya Rike A Rayuwarsa!
Malam Muhammad Danjuma Katsina ya rike mukamai masu yawan gaske a rayuwarsa.Ga kadan cikin su:-
1. Shi ne jami’in hulda da jama’a na kungiyar Marubuta ta kasa (ANA) reshen Jihar Katsina.
2.Ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kungiyar ‘yan Jarida ta kasa (NUJ) reshen jihar Katsina.
3.Ya taba rike Kantoman kungiyar masu shirya Fina-finan Arewa (MOPPAN) reshen Jihar Katsina.
4.Shi ne wakilin gidan Rediyon Iran sashen Hausa na farko a Nijeriya (IRNB).
5.Shi ne mataimakin Editan Jaridar Almizan da ta dauki shekaru 30 ta na fitowa ta Hausa a duk sati a Nijeriya ba tare da ta yi nasan ba.
6.Shi ne mawallafin Jaridar Taskar Labarai ta Hausa da ake gudanar da ita a Internet wacce ta ke da mabiya sama da Dubu 80 a yanzu haka.
7.Shi ne Mallafin jaridar ‘the Links’ ta Turanci wacce ake gudanar da ita a internet al’umma na gamsuwa da rahotannin ta.
8.Shi ne mai shafin Hantsi na jaridar Almizan,da shafin rubutu da Marubuta da ya shafe fiye da shekara 28 ana buga su.
Tsakure Daga Rubuce-Rubucensa
Mal.Muhammad Danjuma Katsina ya rubuta littafai ga kadan daga cikinsu:-
1.Littafin Bosniyya Ta’addancin da aka yi wa Musulmai.
2.Ya rubuta wani littafi a kan Tauhidi.
3.Littafin labarin zube mai suna Yadda ya so wanda an fassara shi zuwa Larabci.
4.Littafin Dan makaranta ya rubuta shi ne a kan zamantakewa da tarbiyya.
5.Littafin Wurare masu Tarihi da albarka a Makka da Madina.Ya rubuta shi a salon hotuna kayatattu da suke dauke da Tarihin wurare masu albarka a Makka da Madina mai shafuka 162.
Mukalolin Da Ya Rubuta A Jaridu!
Hakika Malam Muhammad Danjuma Katsina ya kasance gogaggen Dan Jarida,kuma shaharren Marubuci da ya rubuta mukaloli masu yawan gaske a Jaridun Hausa da na Turanci.Ga tsakure daga wadancan Mukalolin da ya rubuta a Jaridun Hausa wadanda wasu kuma an Tarjama su zuwa Turanci tattare da buga a wasu a Jaridun na Turanci:-
1.Fassara da yadda ake yin ta.
2.Gari ba Kano ba dajin Allah.
3.Allah ya tsare mu daga soki da bishewar albarka.
4.Alhaki kwikwiyo ne bi yake..
5.Duniyar Aljanu.
6.Abunda da suka rasa ya sa suke kisa.
7.Wayyo Allah Najeriya.
8.Darasi daga yakin Duniya na biyu.
10.Jonathan daya daga cikin shuwagabanni masu hadari a Duniya.
11.Darasin da na dauka daga shugabancin kungiyar ‘yan Jarida.
12.Labarin yaro dan shekara 8 a Yemen.
13.Shekaru 20 dan Jarida a bakin aiki.
14.MD Yusuf bankwana da kundin Tarihi mai rai.
Wannan kadan kenan daga tsakuren mukalolin da ya rubuta a Jaridu.
Malam Danjuma Katsina Dan Jarida A Mu’amala
Hakika Malam Danjuma Katsina ya kasance dan Jaridar da na hadu da shi na yi mu’amala da shi tattare da daukar darussa a rayuwarsa masu yawan gaske ga kadan daga ciki:-
1.Son tallafawa na kasa da shi:Na tuna shekaru 5 da suka wuce a sadda nike son tsunduma fagen rubuce-rubuce da aikin Jarida na fara tuntubarsa domin ya bani shawarwari a kan hakan;gaskiya na same shi mai son ci gaban na kasa da shi.A duk sadda na nemi wata shawara ko karin haske a kan wani lamari da ya shige mini duhu, yakan saurare ni tattare da bayar da lokacinsa mai tsada a gare ni.Nasan akwai mutane masu yawan gaske da ya zamanto musu bangon jinginar hakkakar da burukansu a Duniyar rubutu da aikin jarida.
2.Rashin tsoro wajen gudanar da aiki:Malam Danjuma Katsina ya kasance wanda yake aikata aikin jarida na fadar gaskiya a aikace.A kan wannan kafewa tattare da fafutikar tsage gaskiya ya hadu da fushin Mahukunta da barazanoni daban-daban a rayuwarsa.Lallai ya zamanto samfur ga aiwatar da aikin Jarida a aikace a kasar nan musamman a Arewacin Najeriya.
3.Wadatar zuci:Mal.Danjuma Katsina ya rike mukamai masu yawan gaske,amma ya yi iya kokarinsa wajen kin amfani da mukaminsa wajen neman tarkacen Duniya ko kuma kwadayin wani abu ga kashin kan sa.
4.Iya zamantakewa da al’umma:Hakika ga wanda yake mu’amala da Mal.Dajuma Katsina ko yake da alaka da shi ta kusa da ta nesa,zai tabbatar da ce wa,Mal.Danjuma mutum ne wanda yake kyautatawa wadanda suke tattare da shi.Hakan ya sa manyan ‘yan Siyasa,manyan attajirai,sarakunan Gargajiya,Maluman addinin Musulumci da na Kirista,jami’an tsaro suke da alaka da shi.A gefe guda kuma,Shehunan ilimi da suka hada da Farfesoshi,Daktoci,Likitoci suke mu’amala da shi kai tsaye cikin kyautatawa da dattako.Irin wannan kyautata mu’amalar da al’umma ta sa a sadda Mahaifiyar Malam Danjuma Katsina Hajiya Rabi’atu ta rasu a ranar Lahadi 14/6/2020 daidai da 23 ga Shawwal,1441 dimbin mutane suka yi tururuwar zuwa yi masa ta’aziyya ga kadan daga cikinsu;-
Bangaren Malamai
1.Malam Yakubu Yahaya Katsina,Limamin Masallacin Juma’a na Katsina,Shaikh Munir Ja’afar,Shaikh Muhammad Hadi Balarabe,Shaikh Mal Iyal Gafai.
Bangaren ‘yan Siyasa kuwa ga su kamar haka:-
Gwamnan Jihar Katsina,Rt Hon.Aminu Bello Masari,Mataimakinsa Alhaji Mannir Yakubu,babban Daraktan yada Labarai na Gwamnan Katsina Alh Abdu Labaran,shugaban Jam’iyyar PDP na Katsina Hon.Salisu Yusuf Majigiri.
Haka bangaren manyan ‘yan kasuwa sun hada da Alhaji Nafi’u Sani,Shugaban Dadin Kowa store,Alhaji Adamu Lamama shugaban kamfanin burudin Lamama.
Bangaren Malaman Jami’a da Kwalejoji kuwa akwai Shugaban horas da Malamai ta Katsina,Farfesa Idris Maikaji da wasu jami’ansa,Shugaban makarantar kimiyya da fasaha ta Hasan Usman da Jami’ansa,Farfesa Bichi mai rikon Jami’ar Dutsin Ma,Farfesa Abdullah Uba Adamu,Shugaban budaddiyar Jami’ar Najeriya,Dakta Bashir Abu Sabe da abokansa.
Sannan ya samu ta’aziyya daga kungiyoyin Katsina guda ashirin da uku.Kowanne sun turo wakilin wakilansu suka zo,wasu har da rubutacciyar takarda.
Haka bangaren Sarakuna akwai mai martaba Sarkin Katsina,Alhaji Abdulmumini Kabir Usman CFR ya aika tawagar ta’aziyya,haka tsohon Sarki Muhammad Sanusi ll ya turo tawaga daga Legas.
Wadannan bayin Allah da muka lissafo a sama kadan,yana bayyana kyawun mu’amalar da Mal.Muhammad Danjuma Katsina yake yi da al’umma.
Allah ya kara masa lafiya,aminci ya kuma albarkaci rayuwarsa da zuriyarsa ameen.

Exit mobile version