A cikin makon nan ne, gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2026 na kimanin naira miliyan 897,000,000:00, inda ya zama doka domin fara aiwatar da shi.
Kasafin kuɗin da aka yi wa take da cewa “Kasafin Kudin da Jama’a Suka Tsara da Kansu” ta hanyar jin irin buƙatunsu wanda ita kuma gwamnati za ta aiwatar bisa doka.
- Gobara Ta Yi Ajalin Mutum 5 ‘Yan Gida Ɗaya A Jihar Katsina
- Gwamnatin Katsina Da UNICEF Za Su Yi Wa Yara Miliyan 2.8 Allurar rigakafi A Katsina
A iya cewa Gwamna Raɗɗa yana daga cikin gwamnonin arewacin Nijeriya da suka zama na farko da suka gabatar da kasafin kuɗn shekarar 2026, sannan aka kammala kare kasafin kudin a cikin kwanaki 24 na aikin a gaban zauren majalisa.
A wannan kasafin kuɗin, akwai abubuwan da yawa da suka sha bamban da sauran kasafin kuɗaɗen da aka saba aiwatar a gwamnatance, musamman a Jiha Katsina da take da ƙarancin samun kuɗaɗen shiga.
Yana da kyau al’umma su gane cewa gwamnatoci na aiwatar da kasafin kuɗin yadda suka ga dama kuma yadda suke so, saboda doka ta ba su damar haka, sai dai wani abin da ba a saba gani ba shi ne, bai wa jama’a dama su bayyana abubuwan da suke so gwamnati ta yi masu.
Abu na farko da za a duba a cikin wannan kasafin kuɗi har na naira biliyan 897,865,078,282.05 wanda gwamnatin ta dage cewa jama’a ne da kansu suka shirya shi kuma suke san gwamnati ta aiwatar masu da shi.
Wannan shi ne kasafin kudi mafi girma da yawa a tarihin Jihar Katsina, kuma idan ta tabbata cewa na jama’a ne an yi bisa abin da jama’a suke so, to lallai abubuwa da yawa za su canza ta fuskar tattalin arziki da ci gaban al’umma da sauran ɓangarori.
Abu na biyu kan wannan kasafin kuɗi shi ne, zargin da ake yi wa sauran gwamnoni shi ma Malam Raɗɗa bai wuce shi ba, domin ana zargin cewa shekarar zaɓe ta zo za su yi amfani da wannan damar wajen samarwa da kan su kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe.
Abu na uku shi ne, gaba ɗaya kasafin kuɗin na naira biliyan 897,865.000 kashi 18 ne kaɗai zai tafi wajen harkokin gudanarwa kuma shi ne mafi ƙarancin da aka taɓa yi a tarihin Jihar Katsina.
Haka kuma wani sabon tarihin da za a sake kafawa shi ne, kashi 81 na kasafin kuɗin zai tafi ne a manyan ayyuka da gwamnatin Jihar Katsina ta ce jama’a ne da kan su suka zaɓi a yi masu haka.
Abu na huɗu shi ne, har zuwa yanzu babu gundarin kasafin kuɗin a hannun jama’a balanta a ga irin buƙatun da aka fi so da kuma begen a yi a wannan jiha da kowa ya yi imanin cewa kawar da matsalar tsaro ita ce baban abin da jama’a suka fi so a yi masu.
Idan aka duba daftarin kasafin kuɗin 2026 za a ga cewa ba a bai wa ɓangaren tsaro wani kaso mai tsoka ba duk da cewa idan harka ta shafi tsaro ana ƙoƙarin ɓoye ta, saboda harkar tsaro harka ce ta gwamnati kawai.
Abin da masana ke cewa shi ne, idan har babu tsaro duk waɗancan abubuwa da aka lissafa su, ba za su samu ba sai da tsaro, to amma an ce al’umma ta zaɓi wani abu fiye da tsaro da ya raba su da gidajansu da iyalansu da dukiyoyinsu.
Abu na ƙarshe shi ne, Gwamna Raɗɗa ya tabbatar wa jama’a cewa aiwatar da kasafin 2026 zai kasance cikin lokaci, a fili, kuma bisa buƙatunsu. Ya ƙara tabbatar da samar da ci gaba a fannin tsaro a Katsina domin samar da zaman lafiya.
A iya cewa wannan ikirarin da gwamnatin Malam Raɗɗa ta yi shi zai zame mata zakaran gwajin dafi da zai jagoranci samun nasarar gwamnatinsa ko akasin haka.?














