ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Katsina Da UNICEF Za Su Yi Wa Yara Miliyan 2.8 Allurar rigakafi A Katsina 

by El-Zaharadeen Umar
9 months ago
Katsina

Asusun tallafa wa ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) da gwamnatin Jihar Katsina za su jagoranci shirya gangamin yi wa yara miliyan 2.8 allurar riga-kafin cututtuka daban-daban a Jihar Katsina.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da aka nuna buƙatar iyaye da kafafen yaɗa labarai da masu ruwa da tsaki da su ba da goyon bayan domin samun nasara.

  • Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
  • Wuta Ta Ƙone Miji, Mata Da Ƴaƴansu Ƙurmus A Katsina

Shugaban asusun UNICEF na ofishin Kano, Rahama Mohammed Farah ya buƙaci haka a lokacin wata tattaunawa da manema labarai a masaukin baƙi na Albustan Hotel da ke Katsina

ADVERTISEMENT

Kazalika, Rahama ya yaba wa gwamnatin jihar bisa irin gagarumin ci gaba wajen yaƙi da cutar shan inna da take yi, inda ya ce yanzu an samu nasarar da kusan Kashi 90 cikin ɗari.

A cewarsa, asusun UNICEF na sane da irin gudunmawar da kafofin yaɗa labarai suke bayarwa wajen wannan muhimmin aiki, wanda ya ce za su ci gaba da gangami domin tabbatar da samun ingantaciyar kiwon lafiyar al’ummar jihar Katsina.

LABARAI MASU NASABA

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

Shugaban asusun UNICEF na ofishin Kano ya ƙara da cewa rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa tana da muhimmanci sosai musamman a kafafen sada zumunta na soshiyal midiya wajen faɗakar da al’umma kan su kai ‘ya’yansu allurar riga-kafi.

Tunda farko da yake jawabi, shugaban hukumar lafiya a matakin farko na Jihar Katsina, Dakta Shansudeen Yahaya ya sake tabbatar da ƙudirin gwamnatin Jihar Katsina na ƙare lafiyar ƙananan yara a faɗin jihar.

Dakta Shansudeen wanda ya samu wakilcin Dakta Mukhtar Mahmud ya bayyana wannan gangami da za a yi da cewa zai haɗa ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina.

Ya ce akwai muhimman abubuwa da za a gudanar da suka haɗa da riga-kafin shan inna da riga-kafin cututtuka na yau da kullum da rarraba magunguna da bayar da sinadarin Ɓitamin A da taimakon lafiyar uwa da jariri.

Taro dai ya samu halartar masu ruwa da tsaki kan harkar kiwon lafiya da suka haɗa da babban mashawarcin ƙasa kuma shugaban foliyo, Dakta Suleiman Haladu da shugabannin foliyo na sashin bayar da agajin gaggawa da sauran ƙwararru waɗanda suka jaddada buƙatar haɗin kan al’umma domin samun nasara.

Katsina
El-Zaharadeen Umar
+ postsBio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Cutar Mashako:Yadda Yara Ke Mutuwar Bazata A Jihohin Katsina Da Kano
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mauludin Annabi (SAW): Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Addu’o’in Nasara Kan Matsalar Tsaro
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Shekaru 8 Cikin Raɗaɗi: Wani Bawan Allah Ya Samu Tiyata Kyauta Daga Gidauniyar Mangal
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Nemi Malamai Su Taimaka Wajen Yaƙi Da Ƴan Ta’adda

MASU ALAKA

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato
Manyan Labarai

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Next Post
Bam Ya Kashe Matasa 4 A Garin Banki

Bam Ya Kashe Matasa 4 A Garin Banki

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.