Ranar 12 ga watan Janairun shekara ta 2024 da muke ciki, Shugaba Bola Ahmed Tinubu; ya nada shahararren jarumin fina-finai na Kannywood, Ali Nuhu; a matsayin Shugaban Hukumar Shirya Fina-finai ta Nijeriya (Nigeria Film Cooperation).
An kafa wannan hukuma ta shirya fina-finan Nijeriya, a shekarar 1979; karkashin doka mai lamba 61 na kundin tsarin mulkin Nijeriya, wadda aka dorawa alhakin sarrafa fina-finan Nijeriya.
- Yadda Mata Ke Daukar Yara Don Taya Su Aikin Gida
- Gwamnatin Sakkwato Ta Kaddamar Da Gangamin Sa Yara A Makaranta
Har ila yau, a takaice hukumar na aiki ne a matsayin cibiyar gwamnatin tarayya; wacce aka dorawa dukkanin wani alhakin ganin masana’antar ta tsayu da kafafunta tare da fitar da kyawawan halaye da al’adun ‘yan Nijeriya a idon duniya.
Kazalika, Ma’aikatar Yada Labarai da Al’adu ta Tarayya ce ke kula da ita tare da ba ta dukkanin wani iko da take bukata, domin bunkasa al’adu ta hanyar Sinima a Nijeriya.
Ta hanyar ayyukanta, hukumar na bayar da gudummawa kwarai da gaske ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin al’umma, samar da fina-finai don amfanin gida da kuma fitar da su zuwa kasashen waje; na daga cikin muhimman ayyukan da wannan hukuma ke gudanarwa.
Mutuwar Mista Ibu
A ranar 2 ga watan Maris na shekarar 2024, aka wayi gari da labarin mutuwar daya daga cikin manyan jaruman fina-finan Nijeriya (Nollywood) Mista Ibu.
John Okafor Ikechukwu, wanda aka fi sani da Mista Ibu; ya shafe fiye da shekara 40 a masana’antar fina-finai ta Nollywood, inda ya zama guda daga cikin manyan dattijan masana’antar da ake girmamawa; kafin ciwon kafa ya yi sanadiyar mutuwarsa, bayan fama da jinya.
An haifi Mista Ibu ranar 17 ga watan Oktoban shekara ta 1961, a Karamar Hukumar Nkanu West da ke Jihar Enugu, wanda bayan kammala karatunsa; sai ya tsunduma cikin harkar wasan kwaikwayo a shekarar 1978, ya kuma samu shahara a fagen wasan kwaikwayon; musamman a bangaren nishadi a dukkanin bangarorin Nollywood da kuma Kannywood.
Mista Ibu, ya kamu da ciwon kafa da ta kai har ga yanke masa kafar guda daya, an kuma kwantar da shi a asibitin da ke Lekki na Jihar Legas; kafin mutursa a ranar 2 ga watan Maris.
Gwamnatin Kano Ta Gwangwaje Wasu Jaruman Masana’antar Kannywood Da Manyan Motoci
Yayin da wasu ke fita daga tsagin Kwankwasiyya a Jihar Kano suna komawa tsagin APC ta hannun Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin (Maliya), wadanda suka jurewa tsayawa a jam’iyar ta NNPP; sun rabauta da samun kyaututtukan manyan motoci masu tsada da kuma kudade daga Gwamnatin jihar.
Babban mai taimakawa Gwamnan Jihar Kano, a kan harkokin nishadi; Malam Tijjani Gandu ya bayyana cewa, gwamnan ya yi matukar yabawa da irin gudunmawar da jaruman suka ba shi, a lokacin da yake yakin neman zabensa.
Wasu daga cikin jaruman Kannywood, sun samu kyautukan motoci daga wurin Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf; ta hannun babban mai taimaka masa a kan harkokin nishadi, Malam Tijjani Gandu; wannan na daga cikin manyan alheran da jaruman masana’antar ta Kannywood suka samu a wannan shekarar ta 2024, da muke bankwana da ita.
Mutuwar Saratu Gidado
Ranar 9 ga watan Afrilun wannan shekara ta 2024 ne, masana’antar Kannywood; ta wayi gari da mummunan labarin mutuwar daya daga cikin manyan jarumanta mata a masana’antar, Hajiya Saratu Gidado da aka fi sani da Daso.
Labarin rasuwar ya karade gidajen rediyon Kano, inda lamarin ya motsa zukatan jama’ar jihar da ma kasa baki-daya. Marigayiyar ta kwanta da dare, amma Allah bai nufi ta wayi safiya ba,‘yan’uwanta sun ce; ta rasu ne a yayin barcinta na daren Talata, bayan ta ci abincin Sahur. Daso dai, fitacciyar jaruma ce a masana’antar fina-finan Hausa, wacce ta shafe fiye da shekaru 18 a masana’antar.
Adam Zango Ya Zama Darakta Janar Na Gidan Talabijin Kausain
Ranar 8 ga watan Oktoba, Gidan Talabijin Kausain; guda daga cikin rukunin kamfanonin Kausain, ya bayyana wasu sabbin nade-naden da ya yi; domin jagorantar kamfanin a bangarori da dama. A cikin sanarwar Kausain TB, ta bayyana cewa; ta nada fitaccen jarumin fina-finan Kannywood, kuma mawaki Adam A. Zango a matsayin Darakta Janar na gidan talabijin din.
Shugaban Kungiyar Kausain, Alhaji Nasir Idris; a wata sanarwa da bayar a Abuja ya bayyana cewa, nadin Adam Zango a matsayin Darakta Janar; ya fara aiki ne nan take, kazalika a cewar sanarwar; an amince da nadin ne yayin wani taron kwamitin gudanarwa na kamfanin da aka gudanar.
Nan take bayan wannan sanarwa, jarumi Adam Zango; kuma sabon Darakta Janar na Kausain TB, ya wallafa a shafinsa na Facebook; domin ‘yan’uwa da abokan arziki su taya shi murna kan wannan sabon mukami da ya samu. Daga cikin wadanda suka taya shi murna, akwai Shugaban Hukumar Fina-finai ta Nijeriya, Ali Nuhu Muhammad; wanda ya yi masa fatan alheri da addu’ar samun nasara.
Rahama Sadau Ta Samu Mukami A Gwamnatin Tinubu
Har ila yau, a cikin wannan shekara ne gwamnatin tarayya ta nada jarumar Kannywood, Rahama Sadau; a matsayin daya daga cikin shugabannin kwamitin bunkasa tattalin arzikin kasa ta hanyar fasaha da basirar zamani.
Sadau, ta samu wannan matsayi ne; bayan wani zama da suka yi da Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima; tare da sauran manyan mutane a fadar gwamnati, inda aka tabbatar mata da wannan matsayi tare da sauran ‘yan kwamitin.
An dora wa kwamitin, mai suna ‘Inbestment In Digital And Creatibe Enterprise’, hakkin zakulo ‘yan Nijeriya masu fasaha; musamman matasa, domin habaka tattalin arzikin kasa ta hanyar fasaha da basirar zamani a wannan karni.
Mutuwar El-Mu’az Birniwa
Ranar 5 ga watan Disambar wannan shekara ne, mawaki kuma mai shirya fina-finai a masana’antar Kannywood, Mu’azu Muhammad Birniwa, wanda aka fi sani da El-Mu’az Birniwa ya rasu a wani yanayi mai cike da ban tsoro, rahotanni sun tabbatar marigayin na daga cikin ‘yan’uwa da abokan arzikin da suka buga kwallon kafa, domin taya mawaki Auta Waziri; murnar auren da zai yi.
Bayan buga wasan ne, sai •ya nufi asibiti sakamakon rashin jin dadin jikinsa da ya ji, nan take aka kwantar da shi a asbitin; bayan dan wani lokaci ya ce ga garinku. Kafin rasuwar El-Mu’az, ya shahara a fagen wakokin fadakarwa da soyayya.