Kamun Kifi na daya daga cikin manyan ayyukan noma da ke kara yin fice a Nijeriya.
Sana’ar kiwon, ta wuce batun yin ta a matsayin amfan da dabarun gargajiya, wato ta hanyar amfani da Raga a yayin kamun Kifin da kuma amfani da sauran dabarun gargajiya na kamun Kifin.
- Yawan ’Yan Kasashen Waje Da Suka Shigo Kasar Sin Ba Tare Da Biza Ba A Bara Ya Ninku
- Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Kara Haraji Kan Kayayyakinta
A yanzu, akwai hanyoyin zamani na kiwon Kifin a kasar nan, inda a cikin harabar gidanka, za ka iya sayen wani Kwamin adana Ruwa ka rika kiwata su.
Kifi na daya daga cikin hanyoyin da ake samar da abinci a daukacin fadin kasar nan, wanda idan ka je kasuwa za ka ga yadda ake hada-hadar kasuwancin nau’ikan Kifi iri daban-daban da suka hada da danye da kuma wadanda aka yi bandarsu.
Akwai kasuwannin da ake sayar da Kifi da dama a kasar nan, wadanda ake sayar da nau’ikan irin Kifin da mai saye ke bukata.
Bayanai Hudu Da Ya Kamata A Sani Dangane Da Kiwon Kifi A Nijeriya:
1- Kimanin Kashi 40 Kacal Ake Iya Cimma Bukatar Samar Da Shi A Nijeriya:
A cewar wata kididdiga ta Bankin Duniya, Nijeriya a 2018, ta samar da yawan Kifin da ya kai kimanin 1,169,478, wanda ya kai kimanin kashi 40 cikin 100, wanda bukatarsa da ake da ita a Nijeriya a shekara daya, ta kai kimanin tan miliyan 3.4, inda sauran wanda ake bukatar fitarwa waje ya kai kashi 60 cikin 100.
2- Kamun Tarwada A Nijeriya Fitacciyar Sana’a Ce:
Samar da Tarwada a Nijeriya, ya karu daga tan miliyan 21,700 a 1999 zuwa tan miliyan 316,700 a 2015, wanda ya karu da sama da kashi 1,400 a cikin shekaru 25 da suka wuce.
Shugaban kungiyar masu kamun Tarwada na kasa (CAFAN), Cif Tayo Akingbolagun a cikin sanarwar da ya fitar a taron shekara na kungiyar ya bayyana cewa, Nijeriya a 2016 ta samar da sama da tan 370,000 na Tarwada.
3- Nijeriya Ce Ta Uku Kan Gaba A Afirka Wajen Kamun Kifi:
Wani rahoto na 2018 da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa, jimillar Kifin da aka samar a duniya ya nuna cewa, a yanzu Nijeriya ce ta uku da ke kan gaba a Afirka wajen samar da Kifi, inda ta samar da kimanin tan 1,169,478.
4- Kiwon Kifi Na Bunkasa Tattalin Arzikin Nijeriya Da Kashi 3.24:
A cewar wasu bayanai da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar a zango na daya na 2021, fannin Kiwon Kifi ya bayar da gudunmawa ga tattalin arzikin Nijeriya da kimanin kashi 3.24.