Masana sun yi kira da a kafa cibiyar kulawa da lafiyar Hakori a karkashin Asibitin koyarwa na jami’ar Abuja saboda su rika kulawa da matsalolin da ake fuskanta wadanda suke da alaka da fuska da kulawa da maganin cututtukan a Nijeriya.
Sun bayyana irin gudunmawar da kwararrun za su rika badawa ga mutanen da suke fama da cututtukan da suke sanadiyar samar da nakasa da fuska,da suka nuna bukatar a samu wani sashe ko wata cibiyar da za a rika horar da kwararrun da za su rika yin tiyata a fuska ba tare da samun wata matsala ba.
- Bangare Japan Da Ya Dage Sai Ya Zubar Da Dagwalon Ruwan Nukiliya Cikin Teku Zai Sha Kunya Ta Tsawon Tarihi
- Gwamnatin Gombe Ta Sha Alwashin Magance Rikicin Manoma Da Makiyaya
Babban jami’i kuma harila yau shugaban gidauniyar data shafi nakasar fuska shi ne ya bayyana hakan lokacin da ake kaddamar da yin tiyata kyauta ga masu fama da nakasar fuska a Asibitin koyarwa na jami’ar Abuja ranar Talata ta makon daya gabata.
Yace”Da akwai bukatar ba tare da bata lokaci ba kafa wata cibiyar ko makarantar da zata rika kula da lafiyar Hakori a Asibitin koyarwa na Jami’ar Abuja,har yanzu babu irin makarantar ,duk kuwa da yake an fadada makarantar da sauran sassan kulawa da kimiyyar lafiya”.
Ya kara jaddada cewa idan har aka kafa makarantar ko cibiyar ba kawai zata tsaya kan maganin matsalolin da ake fuskanta na rashin kwararru masu tiyatar cututtukan fuska,harma za a bunkasa tsarin da ake da shi na horarwa domin tabbatar da ana da kwararrun da za su kula da cututtukan da suke da alaka da fuska da kokon kai.
Bello ya ci gaba da bayanin cewa karancin kwararrun da suka kware kan cututtukan fuska inda yace “idan an bukatar kulawa wajen maganin cututtukan da suka da alaka da fuska akwai bukakatar ci gaba da samar da kwararru ne na bangaren Hakori wadanda kuma kadan ne a fadin tarayyar Nijeriya,inda ake da ‘yan kada da basu kai 200 ba”.
Bugu da kari ya bayyana cewa “Wannan dubuwar da kulawa da ake yi wa masu nakasar ta 27an samu zuwan mutane da yawa wadanda suke fama da cututtukan da suka shafi fuska daga Jihohi daban-daban,zuwa ranar Talata ta makon daya gabata akwai mutane 44 da suka yi rajista,an yiwa mutane 13 tiyatar yayin da za a cigaba da tiyatar har mako daya ana sa ran za ayi wa mutane 50 tiyatar”.
“Ba zamu iya kulawa ko duba duk masu fama da irin wannan cutar ba sai dai wani abu ne da ke nuna gaskiya ce akwai cutar”
Ya kara yin bayani gudauniyar kungiya ce mai zaman kanta da take kokarin kawar da cututtukan nakasa masu alaka da fuska, a Nijeriya, tana kuma a gaba- gaba wajen wayar da jan al’umma da kulawa da yi masu magani kyauta ta yin tiyata ga masu karamin karfi,zuwa yanzu mutane fiye da 5000 suka amfana da tsarin na kulawa da lafiyar wadanda suke dauke da cutar. Abin daya lura da shi shine samun raguwar masu cutar a Nijeriya.
“Kulawar da aka yi sau hudu manya ne suka mamaye inda ake samun a kallama su shekaru 14.2.Yanzu wadanda cutar tafi damuwa jarirai ne, shine ya bambanta mu da sauran kasashe na duniya inda wadanda ake yi tiyata a fuska yara ne.”
“Yayin da kafa makarantar ko cibiyar kulawa da al’amuran da suka jibanci Hakori a Asibitin koyarwa na jami’ar Abuja zai kara karfafa kokarin da muke yi.Zai bamu damar horar da sabbin kwararrun kulawa da lafiyar al’umma wanda hakan zai kara inganta hanyar samu kulawar data kamata ta wadanda suka samu nakasa a fuksa kamar yadda Bello ya jaddada”.
Da yake jawabi muhimmanci tsarin babban jami’in kulawa da asibitin koyarwa na Jami’ar Abuja Farfesa.Bissallah Ekele cewa ya yi “muhimmancin tsarin bai wuce an kawo farin ciki ga wadanda a baya basu cikin farin cikin saboda nakasar da suke da ita a fuska.Wani abin burgewa shi ne abin kyauta ne aka yi shi abin ai a bayyana yake”. Ya ce irin nau’oin cutar data shafi nakasar fuska ana samunsu a Nijeriya.
Shi ma a nashi jawabin babban jami’in gidauniyar TY Danjuma, Gima Forje,yace suke daukar nauyin yin tiyatar, inda ya kara jadada “ muna taimakawa wajen bada taimako na tiyatar a coci- coci na Nijeriya da wuraren da masu karamin karfi ne za su samu damar kulawa da lafiyarsu kamar yadda ta dace,ya ce sun yi aiki da kwararrun ma’aikata da aka saba yin aiki da su.Shi yasa muke taimakawa kungiyoyi kamar da suke taimakawa wadanda suke bukatar taimakon CFDF.Ka san ba tare da irin tsarin ba na samun mutane wuraren da suke zama ayi masu magani,zai wuya a samu masu nakasar su zo Asibiti ayi masu aiki.”
“Daga karshe ya ce irin tiyatar tana da tsada da wahala yawancin masu fama da cutar basu da hanyar da za su iya samun kudin ayi masu aiki.”