Barista Sunusi Umar Sadik
sunusiayshamohd@gmail.com +23408052923930 (Tes kawai)
Maimaitawa) A ‘yan kwanakin da suka gabata, Majalisar Dattawan kasarnan ta fara bin matakan gyaran Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na shekara ta (1999). Daga abin da muka karanta akwai kudure-kudure kusan talatin da shida (36) wadanda ita Majalisar ta amince da a yi wa wannan kwaskwarima. Daya daga batutuwan da suka fi jan hankali shi ne batun rage shekarun da sai mutum ya kai su ne zai iya tsayawa takara ko dai a mukamin zartarwa, gwamna da shugaban kasa, ko kuma na majalisun taraiya ko na jihohi.
A yanzu dai abin da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya tanada game da shekarun wanda yake neman tsayawa takara shi ne, shekara arba’in (40) ga wanda yake neman kujerar shugaban kasa; shekark talatin da biyar (35) ga wanda yake neman kujerar gwamna ko dan majalisar Dattijai yayin da ake bukatar dan takara ya kai shekaru talatin (30) kafin ya tsaya takarar neman shiga Majalisar Wakilai ta Kasa ko kuma Majalisar Dokoki ta Jiha. An ce shi wannan gyara da za a yi ya rage shekaru biyar ne daga dukkan shekarun da aka ambata. Wato idan gyaran ya tabbata tsarin zai zama shekara talatin da biyar (35) ga dan takarar zama shugaban kasa, shekara talatin (30) ga dan takarar zama gwamna ko Majalisar Dattijai yayin da shekarun shiga Majalisar Wakilai ta Taraiya da Majalisun Dokokin Jihohi zai zama shekaru ashirin da biyar (25) kacal!
Dalili na farko shi ne, su ‘matasan’ tun da fari menene dalilinsu na cewa suna son su yi takara yayin da suke tsakan-kanin shekaru ashirin da biyar zuwa talatin (25-30)? Suna son su shiga a dama da sune su ma su yi ta morewa kamar yadda shugabanci a kasar ya gadar, ko kuma suna so ne a basu dama domin su kai kasar inda su tsofaffin hannun suka gaza kai ta?Idan ‘matasa’ na neman wannan damar ne don kawai su ma su shiga su more, to wannan ba sai an je ko’ina ba, an san abin dariya ne, abin kunya ne kuma abin Allah wadai. Idan kuma ‘matasan’ suna tunanin cewa suna neman a basu dama ne domin yin abin da su wadannan tsoffin hannu suka gaza yi ne, to shima sai muce da akwai sake. Matsalar shugabanci a Nijeriya ba karancin shekarun masu mulki ko yawansu ne ya haifar da ita ba, kuma ba karancin shekarun masu mulkin ko yawansu ne zai kawar da ita dai matsalar ba.
Alal hakika ma in muka yi karatun baya, zamu ga ai su tsoffin hannun da a yanzu ake ganin su suka hana ruwa gudu, sun shiga sha’anin shugabanci da siyasa ne tun da jajayen sawayensu. Haka abin yake tun kafin samun mulkin kai a shekarar 1960; haka abin ya cigaba da kasancewa bayan samun mulkin kan har ma zuwa lokacin kutsen sojoji cikin sha’anin mulki da siyasa, da dawowar mulkin farar hula a lokuta daban-daban.
‘Matasa’ da shekarunsu suka fara daga goma-sha wani abu zuwa ashirin-da sune suka fara kafa jam’iyyun siyasa a kasarnan. Jam’iyyar Matasan Nijeriya, (Nigerian Youth Mobement), da kuma Jam’iyyar NEPU sun ishe mu misali. Mutanen da shekarunsu suka fara daga ashirin da takwas zuwa talatin sune suka fara juyin mulki a kasar nan, kuma su ne suka mulke ta a tsakankanin 1966-1979.
Idan muka dauki shugaban mulkin soja na biyu ma a kasar nan, wato Janar Yakubu Gowon, wanda yayi tsawon shekara tara, ya hau mulkin ne yana dan shekara ashirin da tara (29), a lokacin ko auren fari ma bai yi ba! Haka ma Janar Murtala Muhammad wanda shi kwata-kwata ma rayuwarsa shekara talatin da takwas yayi (1938-1976), amma ya kasance cikin sha’anin shugabancin kasar nan tun yana dan shekaru ashirin da takwas (28), domin kuwa shi ne ma ya jagoranci juyin mulkin watan Yulin shekarar 1966 wanda shi ne ya dora Janar Gowon kan karagar mulkin kasar nan.
Idan muka dawo nan kusa-kusa, wato dawowar mulkin farar hula daga shekarar 1999 zuwa yau, zamu ga ba ta dai sake zani ba. Mafi yawancin wadanda aka dawo fagen dagar da su tsofaffin hannayen ne dai. Idan kuma sababbin shiga ne to za a ga ‘matasan’ ne. In zaa iya tunawa akwai ma wanda ba wai batun yayi takara ba a matsayinsa na matashi, bayan yayi takarar ya samu nasarar lashe zabe, ya nemi shugabancin majalisar wakilai ta taraiya ya kuma samu. Sai bayan zama shugaban wannan majalisar ne aka bankado cewa shekarunshi ma basu kai na ya tsaya takarar ba tun da fari. Wannan ita ta janyo masa ala tilas ya bar majalisar ma gaba daya ba ma kawai shugabancinta ba. Akwai gwamnoni da yawa da suma suna da karancin shekaru matuka gaya lokacin da suka dafe madafun iko bayan kammala zabubbuka a shekarar 1999.
Abin da nake kokarin nunawa anan shi ne, in da ace mika ragamar mulki ga masu karancin shekaru shi ke samar da kyakkyawan shugabanci, to da tuni kasar nan wani zancen muke ba wannan ba. Domin kuwa mun samu shugabanni masu karancin shekaru a yanayi daban-daban (soja da farar hula), a lokuta daban-daban, a kuma matakai da bangarori daban-daban.
Dalili na biyu kuma da zai nuna mana dodoridon batun rage shekarun takara shi ne, wai idan aka yi wannan gyaran hakan na nufin duk dan shekara 25-35 shikenan kawai zai iya fitowa takara ya kuma cimma gaci? Mun sani kwarai ko kusa wannan ba haka bane, saboda ko ma a kasashe da abubuwansu suke tafiya yadda ya kamata, neman shugabanci a tsarin Dimokradiyya irin wacce muke yi abune mai cike da tsatsibe-tsatsibe. Idan har ba yaudarar kanmu za mu yi ba, mun san matashi mai shekaru 25-35 a karan kansa ba yadda zai iya da dawainiyar da take tattare da yin takara. Ko su masu karancin shekarun da muka ambaci sun taka madafan iko a lokacin siyasa, ta da da ta yanzu, sun samu sukunin yin hakan ne saboda samun sahalewar wasu rikakku asha’anin siyasar, abin da ake kira iyayen gida.
Akwai masu ganin cewa za ayi wannan kwaskwarima ne domin su rikakkun na yanzu suna so su budewa ‘ya’yansu masu tasowa kofar shiga siyasa da kuma samun damar mamaye dandamalin takara. Ta iya yiwuwa akwai kanshin gaskiya cikin wannan batu. Domin a gwamnatocin da suka wuce, da ma mai ci yanzu, akwai matan tsofaffin gwamnoni ko dai a majalisun dokoki ko kuma a mukaman minista. Batun kwamishina kuwa ko shugabancin wasu hukumomin gwamnati wannan shi ya fi komai sauki, kuma shi ya fi komai yawa.
Kulle-kulle, makirci da iya tuggu su suka fi yawa da tasiri a siyasa sama da tanade-tanaden dokoki ko kuma Kundin Tsarin Mulki. In muka lura ai zamu ga ana ta korafi kan cewa an danne mata tare da hana musu rawar gaban hantsi a fannin shugabanci da siyasa. Hakan ce ta sa aka samar da wasu manufofi dakuduce-kudurce na kasa da kasa da nufin shigo da matan cikin lamarin amma har yanzu abin ya ci tura. Kwatankwacin hakan shi ne zai faru ga wannan batu na rage shekarun yin takara. Alal hakika ma fa wannan ba wani sabon abu ba ne. Dama haka tsarin yake a can baya. Domin kuwa a karkashin Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na shekara ta 1979 shekara talatin da biyar (35) sune na yin takarar shugaban kasa; talatin (30) sune na yin takarar gwamna da Majalisar Dattijai, yayin da majalisar wakilan tarayya da majalisun jiha mutum zai iya nemansu da zarar ya kai shekaru ashirin da daya (21).Saboda haka in ‘matasa’ suna ganin tafiyar da ake yanzu ba daidai ba ce, kuma kishin kasa da al’ummar kasa ne a gabansu, to ba wannan ce gwagwarmayar da za su yi ba. Sabon shafi za su bude a tsarin siyasar kasar. Su kwace ragamar ta karfi amma ba da tashin hankali ba. Saboda wannan karnin ba karnin tawaye irin wanda aka yi a kasashen China da Cuba da sauransu ba ne a karnin da ya gabata. Za mu fahimci hakan in muka yi duba da abin da ya biyo bayan tawayen da aka yi a kasashen Larabawa irin su Tunusiya, Masar da Libya. In kuma su ‘matasan’ ba zasu iya samar da wannan sauyi ba, to lallai kuwa za su cigaba da zama karnukan farautar su wadannan tsoffin hannun, inda kololuwar mukamin da ‘matashi’ zai iya samu shi ne na P. A. ko kuma S. A.