Aliyu Dahiru Aliyu" />

Mukalar Talata: Cin Zarafin Mata A Yanar Gizo

dahiraliyualiyu@gmail.com                    +2349039128220 (Tes Kawai)

Yanar gizo wani wuri ne mai matukar amfani da yake hada mutane kala-kala masu mabanbantan ra’ayoyi da fahimta a duk fadin duniya. Ina da aboki wanda babban malamine a kasar Amurika da yake turomin litattafai ta imel ba tare da na kashe kudin jirgi don a kawomin litattafai ba. Abu mafi dadi shine ta kafar sada zumunta ta hadani da mutanen da ban yi tsammanin zan gansu a wurin ba. Na yi rijista da makarantu dayawa a intanet kuma na yi kwasa-kwasai a shafukan makarantu. Kai wani sa’ilin idan ina da tambaya wacce na san zan sha wahalar samun amsarta a kusa to kawai shafin “Google Scholar” nake zuwa domin na karanta ra’ayoyin masana akan amsar tambayar. A yanzu ina siyo kayayyaki daga kasar China ko Amurika ta hanyar amfani da wayata ko kwamfuta cikin sauki ina kwance a daki. Kai ko gwamnati nake so ta lura da wani abu ba na jira sai bayan sati daya yazo na turo rubutu a jarida, hawa shafin Twitter dina nake ko Facebook don na nusar da gwamnati cikin sauki. Kai ko jaridu nake son karantawa to shafukansu na yanar gizo nake hawa idan na rasa ta takarda domin karanta labarai. A yanzu nakan karanta mukalun masana a dai-dai lokacin da suka fita cikin sauki ba tare da na jira har sai sun iso Nijeriya a mota ko a jirgi ba. Da ni da yayata da ragowar yan gidanmu duk muna amfani da intanet ta hanyoyi mabanbanta.

Amfani da yanar gizo ko intanet yana daya daga cikin hakkokin mutane, mazansu da matansu. Tamkar yadda kowa yasan tushen hakkokin kowane mutum, na ra’ayi, na addini, na bayyana ra’ayi da sauransu; to haka hakkin amfani da intanet yake. Masu nazari suna ganin cewa tunda rayuwa tana dada zama cakudaddiya da yin amfani da intanet, makarantu da kasuwanni suna kara zama a tafin hannu kuma sada zumunta tana kara karfi ta hanyar yanar gizo; to ba zamu tada samun damar bayyana ra’ayinmu ba matukar an hanamu bayyanashi ta yanar gizo.

A shekarar 2003 anyi wani taro da aka kira “World Summit on the Information Society” a karkashin majalisar dinkin duniya. Bayan hawa da sauka a tsakanin gwamnatoci, kasuwanni da kungiyoyin jama’a sai aka aminta cewa tabbas za’a bar kowa ya yi amfani da yanar gizo domin karfafa hakkinsa na bayyana ra’ayi. A tsakanin shekarar 2009 zuwa 2010, kafar yada labarai ta duniya, BBC, ta yi kuri’ar neman ra’ayi akan amfani da yanar gizo kuma sun samu tabbacin ra’ayin jama’a na kusan kaso 80 cikin 100 akan aminta da cewa amfani da intanet hakkine da ya kamata kowa ya samu, namiji ko mace. Wata kungiyar gamayyar yanar gizo da ake kira “Internet Society” ta yi binciken mutane sama da 10,000 a kasashe kusan 20 ta hanyar yanar gizo kuma ta tabbatar da cewa amfani da intanet hakkine na kowa da kowa. Kaso 83 cikin dari ne suka tabbatar da wannan ra’ayi a yayinda kaso 3 cikin 100 sukace basu da takamaimai akan ra’ayinsu, su kam ragowar kaso 14 cikin 100 sun tsaya tsaka-tsaki ne.

Da haka zamu gane cewa amfani da yanar gizo, ko ta kasuwanci, sada zumunci ko kuma ilimi wani hakkine da ya kamata mata su amfana dashi. Babu dalilin hana mata su amfana da wannan cigaba, kuma kowace hanya wani ya dauka don hanasu amafani da ita, ta hanyar tsoratarwa ko cin zarafi, laifine da yake dai-dai da hana mutum ya bayyana ra’ayinsa kamar na addini ko na siyasa.

To amma akwai babbar matsala. Akwai wadanda suke hawa yanar gizo, musamman shafukan sada zumunta domin su ci zarafin mata ko su hanasu magana a shafin. A yanzu hotuna sun yawaita na mata da ake wulakantawa a shafukan sada zumunta. Mata, musamman a arewacin Nijeriya, suna kokawa sosai kan yadda ake cin zarafinsu a shafukan intanet. Wasu ta hanyar amfani da hotunansu ko kuma a dinga amfani da sunansu wajen yin abinda zai batamusu suna. Wannan itace hanyar da take hana mata amfani da wannan cigaba. Bincike mai yawa ya nuna cewa mata suna fuskantar matsantawa da tsoratarwa ta wajen amfani da intanet a arewacin Nijeriya.

Cibiyar fasahar sadarwa da cigaban jama’a ta CITAD (Centre for Information Technology and Debelopment), ta bayyana cewa abinda yafi bawa mata tsoro a amfani da yanar gizo itace tsoron yanar gizon da abinda zata iya kawomusu a rayuwarsu. Mata suna jin tsoron amfani da intanet saboda yadda wasu suke amfani da abinda zai batamusu domin su ci musu zarafi. Sau nawa zaka ga an dauki hoton mace ana yawo dashi da niyyar cin zarafinta! Kaso 75 cikin 100 na matan da aka zanta dasu a lokacin binciken sun bayyana cewa suna tsoron amfani da yanar gizo saboda tsoron cin zarafi. Kaso 43 cikin 100 na wadanda suke amfani da yanar gizo da aka bincikesu sun nuna cewa suna amfani da intanet da fargaba. Su kam kaso 21 cikin 100 na matan da aka fuskanta da tambayoyi sun nuna kwata-kwata ma basa amfani da yanar gizo!

Yayin da ilimi da kasuwanci suke dada komawa kan yanar gizo, abin takaici ne kwarai ace matanmu suna fargabar hawa intanet saboda tsoron wasu. Makarantu da cibiyoyin bincike, gidajen yada labarai da mujallu duk sun koma shafukan yanar gizo, amma a haka wasu yan tsirarun masu tsoratarwa suna hana mata morar wannan ribar. Matukar ba sake so ake a kara barin matanmu su sake zama koma-baya ta kowace fuska ba, to wajibi ne a dinga barinsu suna hawa shafukan intanet sannan ana kamo masu wulakantasu ana daukan matakin shari’a akansu. Gwamnati sai ta saka hannu akan wannan don a samu da-mai-ido.

Daga bangaren mata, ya kamata su dinga lura da wadanda za su dinga mu’amala dasu a shafukan sada zumunta. Duk da cewa shafukan sada zumunta basu kai kaso 2 cikin 100 na duka shafukan intanet ba, to amma sun fi kowane shafi daukan hankali. Bai kamata mace ta sakankance da wani har ya dinga cewa turamin hotonki babu kaya ajikinki ba don kawai tana tunanin zata aureshi! Bai kamata ko miji ya dinga  daukar hoton matarsa tana tsirara yana ajiye a wayarsa ba. Wani zai iya dauka yaci zarafin matarsa alhalin bai sani ba. Mata su dinga kula da wani irin hoto za su sanya a shafukan Twitter, Instagram ko Facebook. Ki sani daga lokacin da hotonki ya hau shafukan sada zumunta to baki da damar dawo dashi baki daya. Sannan ya kamata mata su san hanyoyin kai karar mai cin zarafi a intanet da kuma rufeshi ruf idan yana kokarin cin zarafinsu.

Su ma maza masu son cigaban yan uwansu mata ba za’a barsu a baya ba. Ya kamata su dinga fadakar da wadanda basu san cewa daukan kowane hoto da yi masa gyararrakin “Photoshop” da kuma watsashi a intanet laifine babba. A gayawa mutane kalmomin cin zarafi da ya kamata su kiyayesu. Kamar nuna cewa mata basu da hankali ko kuma mata basu da tunani da sauransu duk kalmomin cin zarafi ne.

Masu shafukan sada zumunta su dinga daukan matakin gaggawa akan abinda aka turamusu cewa cin zarafine ta hanyar cireshi nan take. Yan sanda su dinga bibiyar shafukan intanet, musamman na sada zumunta, domin su dinga kula da irin wannan munanan aiyuka; amma su kula wajen banbance cin zarafi, bayyana ra’ayi, kawo gyara da kuma kalaman batanci. Ba kowane kawo gyarane kalaman babatanci ba. Kungiyoyi masu zaman kansu su ma ya kamata su dinga karfafawa mata guiwar amfani da yanar gizo da kuma bayyanamusu hanyoyin da zasu rabu da illolin da zasu iya fuskanta a shafukanta.

Exit mobile version