Wannan wata tattaunawa ce da gidan talabijin din ARISE TV ya yi da tsohon gwamnan Jihar Kwara, kuma tsohon shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, DAKTA ABUBAKAR BUKOLA SARAKI, inda ya yi bayani mai tsawo kan irin cancantar tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar ga shugabancin Nijeriya fiye da sauran abokan takararsa a babban zabe mai karatowa. Ga tattaunawar kamar haka:
Shin ta wadanne hanyoyi kake ganin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar zai kai ga samun nasara?
Da farko dai, na yi imanin cewa zaben shekarar 2023 zai zama tamkar bita ne tare da cimma matsaya a kan irin mulkin da jam’iyyar APC ta yi. Kuma na yi imanin cewa, kasa irin tamu wacce take da mutane masu hangen nesa da sanin ya kamata, ba za ta bi bayan gazawa ba. Tambayar da ya kamata ‘yan Nijeriya su yi ita ce: Shin wannan gwamnatin ta jam’iyyar APC ta gaza ko ta yi nasara a sama da shekaru bakwai da ta kwashe tana mulki?
Bari mu yi bita a tsanake na abubuwan sannu a hankali, saboda ina so in yi magana ne tare da kafa hujjoji, ba wai shaci fadi ba. A shekarar 2015, sun yi wa ‘yan Nijeriya alkawurra da yawan gaske, ciki har da cewa za su kawo karshen matsalar tsaro, za su bunkasa tattalin arziki, tare kuma da samar da ayyukan yi ga matasa.
Wadannan su ne muhimman abubuwan. A shekarar 2015, idan ana iya tunawa, ana fama da matsalar tsaro a yankin Arewa- Maso Gabas, amma tun daga wannan lokacin har zuwa yau, mun ga yadda lamarin tsaro ya tabarbare a yankin Arewa- Maso Yammacin Nijeriya. Manoma ba su iya zuwa gonakinsu saboda ana kashe mutane a kuma yi garkuwa da su. Kowa ya shaida rikicin makiyaya da manoma a yankin Arewa ta tsakiya. Haka kuma muna ganin yadda annobar fasa -kwaurin man fetur ta karu a yankin Kudu-Maso-Kudu.
Dangane da tsaro, sun gaza, wannan babu tantama. Mu dau tattalin arziki, shi ma zan dauke shi bi da bi, sannan na kalubalance su a kai. Mu dau batun karyewar darajar naira. A kan batun tsaro, sun gaza. Bari mu duba tattalin arziki kuma zan sake bin su daya bayan daya in kalubalance su a kai saboda duk matakai ne da aka san su matuka gaya. Bari mu duba tsadar kayayyaki, a yanzu haka ana kusan kashi 16 cikin kashi 100, abin da ba a taba gani a zamanin PDP ba saboda bai kai kashi 10 ba. Muna da mafiya yawan ‘yan Nijeriya da suke cikin kangin talauci da fatara su fiye da miliyan 33.
Ba haka lamarin yake a can baya ba…
Rashin aikin yi a karkashin mulkin PDP yana kashi shida zuwa kashi takwas, a yau kuwa yana kashi 33, sai matasa marasa aikin yi da suke da kashi 54. Zuba jari kai tsaye daga kasashen ketare kuwa, idan mun yi sa’a watakila ya kai Dala Biliyan Biyu idan aka kwatanta da Dala Biliyan 9 a lokacin da PDP take mulki. Wannan shi ne zahiri da ko mutum ba ya tsoron Allah ba zai musanta ba.
Me za ka ce a game da halin da tattalin arziki yake ciki?
A tattalin arziki kuwa, a farashin gwamnati, Dala tana a N185, a kasuwar bayan fage kuma N230 a zamanin PDP. A yau kuwa farashin gwamnati shi ne N450 a kasuwar bayan fage N755. Ba a taba ganin hakan ba sai a zamanin APC. Idan ka duba dukkan wadannan abubuwa, za ka ga cewa APC ta gaza, kuma saboda sun gaza a matsayinsu na jam’iyya, bai kamata mu saka musu da abin kwarai ba. Saboda haka ba na tunanin cewa APC wata abar damuwa ce a wannan gwagwarmaya saboda sun samu damar da za su kyautata jin dadin ‘yan Nijeriya, amma kayya! Sun barar da damar.
A yanzun tambayar ita ce, wa zai gaje ta? Wasu za su iya cewa ba ma so mu koma PDP. Amma bari mu yi batun komawa PDP. A zamanin PDP kamar yadda na yi bayani, matsalar tsaro ta takaita ne ga bangare daya kawai na kasar nan. A lokacin PDP, bunkasar tattalin arzikin ta ‘yan Nijeriya tana wajen kashi 8 amma a yanzun dududu ba ta wuce kashi biyu ba, wato kasa da karuwar yawan jama’a da ake samu.
A zamanin mulkin PDP da muke magana a kai, ana zuba jari daga kasashen waje zuwa kasar nan har na wajen Dala Biliyan 8, kuma mu ne muke da tattalin arziki mafi girma a Afirka. Musayar kudi ba N700 ta doshi N1000 a lokaci guda ba. A zamanin gwamnatin PDP, kan kasar nan ya fi zama a hade. Ba sabon abu ba ne a tsari na dimokradiyya jama’a su zama suna da zabin cewa sun gaji da wata jam’iyya za mu gwada wata.
Amma idan sabuwar jam’iyyar ta gaza, sai ka yi abin da ake cewa da tsohuwar zuma ake magani. Wannan tsohuwar zuma kuwa ita ce PDP karkashin Atiku Abubakar. Idan ka yi magana a kan sauran jam’iyyun siyasan, idan ka dauki ‘yan takaran nasu daya bayan daya, musamman Mista Peter Obi, kada a manta cewa muna gudanar da tsari ne na shugaban kasa mai cikakken iko a Nijeriya kuma idan ka je akwatin kada kuri’arka a ranar zabe, jam’iyya za ka zaba ba Peter Obi ba. Ba za ka ga Peter Obi ba, jam’iyyar za ka gani. Jam’iyyar da tun a farkon farawa ba ta da ‘yan takara na dukkan kujerun ‘yan majalisa, wanda tamkar shiga motar da ba ta da direba ne saboda ka san cewa bangaren zartaswar da na ‘yan majalisun ba za su kasance suna da rinjaye ba.
Kuma wasu za su ce ai sun damu da abin da ake kira sake fasalta tsarin da ake ciki. Wadannan abubuwa, suna bukatar sake nazarin tsarin mulkin kasar nan. Wanda kuma sai kana da rinjaye a majalisar dokoki ta tarayya.
Masu zuba jari sun daina gamsuwa da umarni da kuma dokokin da bangaren zartaswa yake yi; suna so su ga dokoki na ‘yan majalisa da za su mara wa zuba jarin nasu baya. Saboda haka idan ke karamar jam’iyya ce, ba ki da rassa da yaduwa da bazuwa kowanne lungun kasar nan saboda mun ga haka a 2015 cewa mu yi nesa-nesa da romon baka zuwa zahiri.
Zahirin kuma shi ne APC ta gaza saboda burin jam’iyyar shi ne cin zabe, amma ba jam’iyya ce da aka ginata da kyakkyawar aniya ba.
Saboda haka karamar jam’iyya da ba ta yadu zuwa sassan kasar nan ba, ko da tana da shugaban kasa, ba ta da ‘yan majalisar dokoki, ba za mu ga abin da ‘yan Nijeriya suke bukatar gani ba.
Dokokin da za su canza tsarin mulki, su sauya fasalin tsarin da kasar take gudana, majalisar dokoki ta kasa ce kawai za ta iya yi.
Wannan ya kai ni ga batun Atiku Abubakar, a Atiku Abubakar, kana da dan takara da tun daga ranar farko, a shirye yake. Za ka ga me nake nufi da hakan. Yana da kwarewa har a matakin tarayya ba a dan karamin yanki ba. Sauran ‘yan takaran biyu kuwa kurewarsu ke nan ta sun yi gwamnoni a dan karamin yanki. Ni ma na yi gwamna sai dai zan fada muku abin da na sani a matsayina na gwamna tsawon shekara 8, da kuma kwarewata a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa, da nake shugabantar ‘yan Nijeriya daga sassa daban-daban na kasar nan, harsuna daban-daban, addinai da al’adu daban-daban. Ba ka da wannan ilimi ko kwarewa a matakin dan karamin yanki na gwamna.
Wasu suna cewa idan mutum yana so ya lashe zaben shugaban kasa, dole ya samu nasara a wasu jihohi, kana ganin PDP ta yi isasshen abin da ya kamata ta yi domin yaduwar da ake bukata?
Amsa ce mai saukin, PDP a matsayinta ta jam’iyya da take da irin dan takaran da muke da shi a Atiku Abubakar, za mu yi saukin samun kashi 25 da tsarin mulki ya bukaci a samu daga sassan kasar nan. Duk wani hasashe da tattaunawar da za ka yi a kan haka, za ka ga cewa mun zo na farko ko na biyu. Kudu-maso-kudu yanki ne da PDP take da karfi kuma za mu taka rawar gani sosai a can.
A Kudu -Maso-Gabas, kalubalen da ke gaban mu bai wuce na jam’iyyar Labour Party. Duk da haka za mu taka rawar gani a shiryar mu samu kashi 25 dinmu. Za mu taka rawar gani a Arewa-Maso-Tsakiya ma. Haka nan a Arewa-Maso- Yamma da Arewa-Maso-Gabas. Kana bukatar shiyyoyi hudu ka lashe zaben. Shiyyoyinmi guda hudu za su kasance Arewa-Maso-Yamma, da Arewa-Maso-Gabas, da Kudu-Maso-Kudu da Arewa-Maso-Tsakiya kuma za mu samu kashinmu 25 a fiye da jihohi 24. Ba wata tantama ko tababa a kan haka.
Sai dai tsarin da kake batu a kai, shi ne dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party Peter Obi ya ce yana so ya rusa…
Za ka iya watsi da tsohon tsari amma ya kamata ya zama wanda za a fahimta. A kasar Faransa, lokacin da Shugaba Macron ya hau, ba ya cikin tsarin sake fasalin, sai dai tafiyar ba ta bangaren zartaswa ne kawai ba, kasar ta zabi ‘yan majalisar dokoki na jam’iyyar ne. Ba wai ina nufin akwai wata matsala da hakan ba ne. Abin da nake cewa shi ne a jam’iyyar an fi ba da fifiko ne ga shugaban kasa.
Dole tafiyar ta zama har da majalisun dokoki na jihohi da na tarayya. Jam’iyyar da ba ta da ‘yan takaran majalisun dokoki tun farkon farawa, yana nufin an fara saka da mugun zare ke nan. Wannan yana nuna gwamnatin ba za ta gudanar kamar yadda ya kamata ba ke nan. Saboda ba za ta samu goyon bayan da ya kamata a ce ta samu ba, domin iya gudanar da tsare-tsarenta da kuma manufofinta.