Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa, CGI Isah Jere Idris ya bayyana cewa sun duƙufa a kan tabbatar da tsaron iyakokin Nijeriya da ya kai tsawon kilomita sama da 5000 a sassan ƙasar domin zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
Ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Jihar Jigawa a yau Asabar domin ta’aziyya da kuma jaje ga jami’an hukumar da ‘yan bindiga suka kai wa hari a ranar 9 ga Agustan 2022.
A wani jawabi da ya yi wa manema labarai, CGI Isah Jere ya bayyana cewa, “Bari na sake jaddada cewa mun duƙufa a kan tabbatar da tsaron iyakokin ƙasar nan babu fashi, za mu ƙara himma da ƙwazo a wannan bangaren. Za mu cigaba da tabbatar da kare dukkanin iyakokin Nijeriya domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali kasar nan.”
Kwanturola Janar na hukumar ta NIS ya sanar da cewa yanzu haka suna amfani da na’urorin zamani wajen inganta aikin tsaron iyakokin kasa.
Isah Jere Idris ya nemi hadin kan jama’a wajen cimma nasarori kan harkokin tsaro, “Muna neman haɗin guiwar jama’a da ‘yan jarida wajen cimma nasarorin inganta tsaro.”
Ya ƙara da cewa yanzu haka hukumar ta maida hankali wajen amfani da fasahar zamani wajen kyautatawa da inganta tsaro a iyakokin kasar nan.
Jere ya ce ya ziyarci Jihar Jigawa ce domin ganawa da jami’ansa na jihar tare da jajanta wa iyalan jami’insa Abdullahi Mohammed da ya rasu a lokacin da yake bakin aikinsa na kare ƙasa.
“Na zo nan Jigawa domin jinjina irin ƙwazo da ƙoƙari da haziƙancin jami’inmu bisa sadaukar da kai da jarumtarsa wajen kare kasar nan da kiyaye kimarta. Za mu ci gaba da tuna Abdullahi Mohammed a matsayin jarumi kuma haziki. Ina tabbatar wa iyalan mamacin cewa tabbas jininsa bai tafi a banza ba. Muna addu’ar Allah ya jikansa ya gafarta masa.”
A cewarsa: “Marigayi Abdullahi Mohammed da abokan aikinsa suna sintiri ne a hanyar Galadi zuwa Birniwa a ranar 9 ga watan Agustan 2022 yayin da wasu marasa kishin ƙasa suka kai musu farmaki a yayin da suke bakin aikinsu. Shi Abdullahi da abokan aikinsa irin su Abba Musa Kiyawa (DSI) da Zubairu Garba (AII) sun jajirce tare da mayar da martani ga waɗanda suka kawo musu harin, abin takaici ya gamu da raunuka sakamakon hakan ya rigamu gidan gaskiya.”
Kazalika, Jere ya kai irin wannan ziyarar ta jajantawa ga sauran abokan aikinsu biyu da suka gamu da raunuka a sakamakon harin, “Suna amsar kulawar Likitoci a nan Jigawa. Tun lokacin da na karɓi ragamar shugabanci na mayar sha’anin kula da jin daɗi da walwalar jami’aina a matsayin abu mai matukar muhimmanci a tsare-tsarena.”
Shugaban hukumar ta NIS ula ya kuma shaida cewar, kyautata jin dadi da walwalar jami’an hukumar shi ne ya sanya a gaba kuma ya bai wa muhimmanci domin tabbatar da jami’an na samun yanayin gudanar da aiki yadda ya kamata.
Ya ce, yana tabbatar da kula da jin dadin nasu ne domin ba su ƙwarin guiwar gudanar da ayyukansu yadda ya dace don tabbatar da kare kasa a kowani lokaci, “Kuma na himmatu a wannan fannin zan kuma ci gaba tabbatar da jami’aina na samun kyakkyawar yanayin aiki a kowani lokaci.”
Shugaban ya ƙara da cewa irin wannan kulawar tasa ce ma ta sanya shi da kansa ya kai ziyarar ta’aziyyar jami’insa da ya rasa ransa a fagen aiki tare da ziyarartar wadanda suka jikkata a gadon asibiti duk da tarin ayyukan da suke gabansa amma ya jingine su don kai wannan ziyarar.
A wani labarin kuma wani kamfanin da ke harkar ƙawance da hukumar ta NIS wato Contect Global Services Ltd ya ba da tallafin naira miliyan huɗu (N4,000,000) ga iyalan mamacin da kuma wadanda suke jinya.
CGI Isah Jere dai ya sake nanata aniyar NIS ta ba da muhimmanci sosai ga tsaron iyakoki domin tallafa wa tsaron ƙasa da samun ci gaba mai ma’ana.