Connect with us

TATTAUNAWA

Mun Kafa ‘JDSC’ Don Wanzar Da Zaman Lafiya Ne – Rabaran Henry

Published

on

RABARAN FATHER HENRY KABANG shi ne Ko’odonetan wata kungiya mai rajin samar da zaman lafiya a tsakanin jama’a ta ‘Justice Development And Social Cohesion Initiative’ da ke aikin karfafa zaman lafiya a jihohin Bauchi da Gombe. A wani taron zaman lafiya mai taken ‘Peace Ambassador Summit 2020’ da su ka shirya tare da gudanarwa a Bauchi, Wakilin LEADERSHIP A YAU, KHALID IDRIS DOYA ya tuntube shi, don jin manufofin kungiyar nasu ta JDSC, inda ya ke mai shaida cewar da zaman lafiya ne kowane irin cigaba ke samuwa.

 

Ka gabatar ma na da kanka?

Rabaran Father Henry Kabang, wanda nake aiki da wannan kungiyar ta JDSC mai rajin samar da zaman lafiya a jihohin Bauchi da Gombe.

 

Mene ne manufar shirya wannan taron bita wa Musulmi da Kirista?

Manufar wannan kungiyar shine lalubo hanyoyin da za mu tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da salama tare da ganin yanda Musulmi da Kirista za su zauna tare babu wani matsala na rashin jituwa. Mun san yanzu akwai zaman lafiya a tsakanin addinai amma yana da kyau mu karfafi juna kan muhimmancin zaman lafiyar ba wai sai rikici ya tashi kafin mu kira mutane su zo a inganta zaman lafiya ba. A kowani lokaci yana da kyau a zo a zauna mu tunasar da kanmu abubuwan da ya kamata mu sani da kuma abubuwan da suka dace mu bi domin zaman lafiya ya ke habakuwa. Akwai gayar muhimmanci ga fadakar da jama’a muhimmancin zaman lafiya domin kyautatuwar zaman lafiya a tsakanin jama’a.

 

Akwai matsalolin tsaro da suka yi wa kasar nan katutu kama daga fashi da makami, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, shin da irin wannan taron naku kana ga za a samu natija wajen shawo kan matsalar nan?

 

Tabbas da irin wannan tarukan za a samu mafita da gyara matuka, idan ka lura da jawaban da wadanda muka gayyata suka yi, musamman shi babban dan sandan da ya gabatar mana da makala, ya wayar da kan mutane yadda jama’a da kuma su ‘yan sandan za su hada kai domin yin aiki tare wajen dafa wa ta fuskashin shawo kan matsalolin tsaro duk da ka zayyana din nan. Jami’an tsaro suna matukar bukatar hadin kan jama’a ta fuskacin kai rahoton dukkanin motsin wani ko wasu da mutane basu gamsu da su ba; idan ka kai rahoton abin da ke faruwa ga jami’an tsaro ba za su bayyanaka ba, za su boye sunanka da kanka kuma za su binciki abin da ka sanar musu idan na daukar matakin gaggawa ne za su bi har a samu gyara ko dakile wani matsalar.

Shi dan sandan da ke jawabin nan ya shaida wa jama’a cewa dan sanda abokin kowa ne, ya kamata mu ke sanar da su bayanan na zahiri da na sirri domin zaman lafiya yake ingantuwa. Idan ka fadi abu za a bi idan ya tabbata gaskiya ne za a yi aikin da ya dace a kai. Don haka jama’a su rungumi hulda da jami’an tsaro wajen basu bayanai da kai rahoton duk abin da ke faruwa da su.

 

A daidai lokacin da kake neman jama’a su ke rungumar hulda da jami’an tsaro, su kansu jami’an tsaron nan ana zarginsu da tauye hakkin jama’a ta ya kake kallon jama’a za su sake fuska wa jami’an tsaro a irin wannan bigiren?

A gaskiya mu dai muna kokarinmu wajen ganin an samu daidaituwa kan lamarun tsaro. Muna kan namu kokarin, a daidai lokacin da muke fadada mu’amalarmu da su jami’an tsaron za mu nazarci yanayin tafiyar da mu’amalar idan mun ga rashin daidai za mu nusar da yadda za a yi domin a samu gyara. Don haka aikin da ke gabanmu na da girma don haka muna kai kuma tabbas za mu yi kokarin ganin an samu gyara mai ma’ana.

 

Akwai wasu kungiyoyi masu irin wannan manufar taku, akwai shirin hadaka da su ne?

Mun dai fara kokarin cimma namu manufar, na kuma san akwai wasu kungiyoyin da suke da irin wannan manufar su ma suna kan nasu; aikin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin jama’a aiki ne na hada karfi da karfe, don haka za mu jawo kungiyoyin da su ka dace domin mu tafi tare wajen kyautata zaman lafiya a tsakanin jama’a. Za mu hada kai da kungiyoyi ba kawai a cikin Bauchi ko Gombe ba, har sauran jihohin da suke kasar nan zamu shiga domin tabbatar da hakarmu ta cimma ruwa.

 

A wannan taron da ku ka yi a Bauchi mutane nawa ku ka gayyata?

Mahalarta wannan taron bitar sun fito daga jihohin Bauchi da Gombe da yawansu ya zarce 50. Kuma mun zabo sune daga kananan hukumomi daban-daban na wadannan jihohin, don haka a cikin jihohi biyun nan kusan kowace karamar hukuma ta na da wakilci a wannan taron bita kan hanyoyin da za a kyautata zaman lafiya a tsakanin jama’a.
Advertisement

labarai