Gwamnatin Kano ashirinta na bayar da Ingataccen Ilimin bai daya, ta bayyana cewa ta kashe kimanin Naira Biliyan 7 a bangaren Ilimi.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka a jiya Talata a taron zangon shekara na biyu na Hukumar Ilimin bai daya (UBEC) tare da shugabannin zartaswa na Hukumar.
Taron an gudanar da shinene a dakin taro na Africa House da ke garin Kano. Inji rahoton Kamfanin jaridar labaran Hausa.
Ganduje ya bayyana cewa, sabida magance matsalar rashin zuwan yara makaranta, gwamnatinsa ta yanke shawarar baiwa yaran Ilimi kyauta kuma wajibi yaran su dinga zuwa makaranta musamman ‘yan mata da kananan yara.
Gwamnan, wanda ya sami wakilcin mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna,ya ce manufar samar da shirin ya ta’allaka ne domin ganin an magance matsalolin rashin zuwan yaran makaranta musammana ‘ya’ya mata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp