Wata kungiyar APC ta yi kira ga shugaban jam’iyyar na kasa da dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Ahmed Bola Ahmed Tinubu da su dauka gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani-Bello a matsayin mataimakin Tinubu.
Jam’iyyar dai tana da kasa da kwanaki biyu ne kacal don yanke shawara kan wanda zai zama mataimakin dan takarar shugaban kasan.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Laraba a Abuja ta hannun kodinetan jam’iyyar APC na kasa kuma sakataren jam’iyyar Patriots na kasa, Prince Zadok Bukar da Cif Omini Ofem, kungiyar ta ce: “kiranta na a dauki gwamna Sani Bello a matsayin mataimakin Tinubu ya ta’allaka ne a kan ayyukansa.
“Gwamna ne da ya samu karbuwa a wajen takwarorinsa da ’yan Nijeriya, fahimtarsa da adalcici da daidaito da kuma gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban APC a matsayin jam’iyya mai mulki.”
Sanarwar ta ce Gwamna Sani-Bello ya yi fice ne da “halayensa na tausasawa, Wanda ke hada mutuntaka tsakanin matasa da iyaye, Mai daraja addinatai ne, mai cikar lafiya ne, mai cikakken tunani ne kuma mai hada tarayya ne tsakanin yankin Arewa da Kudu.
“Donhaka lallai wannan matsayi ya dace da shi.”