Connect with us

LABARAI

‘Mun Samu cinikin Raguna A Bana’

Published

on

Sakataren kungiyar masu sayar da raguna na jihar Legas, Alhaji Gabcami Mohammed Jidda dake a karar Basi ta Isheri a kusa da bega ta jihar Ogun, ya bayyana cewa, duk da hakin matsin tattalin arzikin da ake fuskanta a kasa a wannan shekarar sun samu cinikin raguna yadda ya kamata, Alhaji Gabcami ya yi wannan furuncin ne a yayin da yake tattauna da manema labarai ofishinsa ciki har da wakilinmu. Ya kuma wara da cewa, an shigo da dabbobi daga Arewacin kasar nan da kuma kasashen makwabta.
Ya kuma lura cewa, a wannan shekarar mutane sun sami zabin sayen raguna daidai karfinsu, domin kuma in har mutum ba zai raina ba har ragon dubu 10 ana samu a cikin ragunar da ake sayarwa, ya kuma ce a wannan shekarar sun samu nasarar sayar a ragon daya kai na Naira dubu 400, an kuma sayar dana Naira dubu 300 dana dubu 150 da sauransu.
Alhaji Gabcami ya kuma bayyana cewa, a wannan shekarar, ‘yan siyasa da manyan masu kudin jihar Legas sun yi azama wajen sayan raguna don rarraba wa mutanesu, wannan kuwa yana faruwa ne musamman saboda ganin an dumfaro kakar zaben 2019, daga nan ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa dasu rage buri a yayin sayar da dabbobinsu, yin haka zai sa koka ya samu, su kuma su samu albarkar sosai, ya kuma yi fatan al’umma musulmi za su yi bukin sallah lafiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: