Mun Shirya Tsaf Domin Kyautatawa Masu Zuwa Aikin Umura

MECCA, SAUDI ARABIA - SEPTEMBER 2: Muslim pilgrims circumambulate around the Kaaba, Islam's holiest site, located in the center of the Masjid al-Haram (Grand Mosque) in Mecca, Saudi Arabia on September 2, 2016. ( Orhan Akkanat - Anadolu Agency )

Kamar yadda kamfanonin shirya tafiye tafiye zuwa aikin Umura kasar Saudiya ko kuma zuwa kasashen waje hutun karshen shekara da sauran su.

Shima za’a iya cewa kamfanin shirya safiye tafiye mai suna Hamsly Trabel and Tour dake Kano ya kammala shiri domin fara jigilar masu zuwa aikin Umura kasar saudiyya muasamman wadanda za su tafi ta kamfanin shi, kamar yadda babban manajan daraktan Alhaji Mustapha Hamisu ya shaidawa manema labarai haka kwanakin baya a garin Kano.

Manajan Daraktan ya ce wasu daga cikin shirye shiryen suna hada da samar masu da masaukai masu kyau da inganci tare kuma da kula da lafiyar su . Haka kuma an samar masu da motoci da za su rika jigilar su zuwa wuraren ibada akan lokaci batare da matsala ba.

Baya ga masu zuwa aikin ibadar kasar Saudiyya hatta masu zuwa wasu kasashen Duniya domin hutun karshen shekara suma an yi masu tanadi.Daga nan sai ya yi kira ga masu irin wadan nan kamfanoni shirya tafiye tafiye cewa su tabbatar sun tsare gaskiya da amana , matukar mutum ya ba ka aiki ka tabbatar ka yi yi ma shi aiki tsakani ga Allah ba tare da yaudara ba .

Alhaji Hamisu Gwaram, ya ce kamfanin su yana bakin kokari wajen kiyaye dokin kasar  Saudiyya da na kasar nan da kuma duk inda suke kai matafiya. Sannan kuma kamfanin s u ba ya gudanar da aiki ga duk wanda suka fahimci ba shi da gaskiya musamman zuwa aikin Umura ko Hajji.Daga karshe ya godewa daukacin manya da kana nan ma’aikatan kamfanin a bisa hadin kai da goyon baya da suke baiwa kamfanin musamman lokutan aikin Hajji da Umura.

Exit mobile version