A jiya Alhamis ne Sarkin Potiskum ta jihar Yobe, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, wato Mai Pataskum ya kawo ziyarar ta’aziyya zuwa Hedikwatar jaridar LEADERSHIP domin ta’aziyyar rasuwa Marigayi Sam Nda-Isaiah, inda a cikin jawabinsa gaban ’yan uwan Marigayin, tare da sauran ma’aikatan kamfanin, Mai Pataskum ya bayyana cewa ya zo ne domin a yi wa juna ta’aziyya, “domin Sam xan mu ne, mu ma mun yi matukar rashinsa,” in ji Sarkin.
Alhaji Umaru ya ci gaba da bayyana Marigayin da cewa mutum ne mai matukar daraja da girma a masarautar Pataskum, wanda wannan ya sa masarautar ta yi masa sarautar Jakadan Potiskum.
Ya ci gaba dayyana cewa rashin Sam Nda-Isaiah ba wai rashi ne na LEADERSHIP ko iyalansa ko masarautar Bida kawai ba, rashi ne na duk kasar nan baki xaya, musamman bisa la’akari da irin abubuwan da ya sanya a gaba don ciyar da kasar nan zuwa mataki mai nisa.
Don haka ya yi fatan cewa iyalai da jagororin kamfanin LEADERSHIP za su rike amanar da ya bar masu, su tabbatar da cewa abubuwan da ya bari sun xore, kamar yadda ya so ya ga sun ci gaba.