Rundunar sojin Nijeriya ta yi watsi da rahoton ceto Laftanar P.P. Johnson, jami’ar soja mace, wadda haramtacciyar kungiyar IPOB ta yi garkuwa da ita a ranar Litinin, 26 ga Disamba, 2022.
Wata sanarwa da Daraktan yada labaran rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar a ranar Juma’a, ta ce an sace ta ne a lokacin da ta ziyarci kakarta a Aku-Okigwe a Jihar Imo, jim kadan bayan ta kammala horonta.
- Nijeriya Ta Yi Haramar Tarbar 2023 Da Harkokin Babban Zabe
- Lardunan Kasar Sin Suna Bunkasa Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Afirka
Faifan bidiyon sace ta ya bayyana a shafukan sada zumunta inda wadanda suka sace ta suka yi ikirarin cewa sace ta ya yi daidai da yakin da suke yi na kafa Kasar Biyafara.
Kakakin rundunar sojin suna fadada bincike don ganin sun ceto ta a kan lokaci ba tare da wani abu ya same ta ba.
Sanarwar ta kara da cewa faifan bidiyon da aka yada ya tada kura.
Nwachukwu, mace ce kuma ‘yar Nijeriyar da ta fito daga yankin Kudu maso Gabas bai hana wadanda suka sace ta su tozarta ta ba a yunkurinsu na ta’addanci da sunan fakewa da kafa kasar Biyafara.