Daga Bala Kukkuru,
Mataimakin Shugaban Kungiyar masu gudanar da harkokin kasuwancin tumatiri da sauran kayan gwari ta kasa Alhaji Malam Hamisu Malam Danja, ya bayyana bukatun kungiyarsu a tsakaninsu da Gwamnatin Tarayyar kasar nan, wajan cigaba da fadada masu harkokin noman rani da damina a Nijeriya da kewayanta baki daya.
Mataimakin shugaban kungiyar, ya yi wannan tsokaci ne a ofis dinsa dake garin Danja jim kadan bayan tashi daga taron su da wadansu kusoshin kungiyar dake cikin garin Danja, a cikin su har da Shugaban kungiyar na Karamar Hukumar Danja Alhaji shafiu Usaini Danja inda Malam Hamisu malam ya cigaba da fashin baki a game da harkokin kasuwancinsu na kayan gwari cewa, babu shakka wannan kungiyar tasu ta masu kasuwancin kayan gwari tana bukatar karin taimako a wajan Gwamnatin tarayya na cigaba da kara fadada masu harkokin noman rani da na damina, domin al’umma su cigaba da samun abubuwan tsayuwa da kafafuwansu.
Sannan ita ma Gwamnatin ta samu sauki a wajan samarwa matasa ayyukan yi a kasar da sauran makamantansu, ya kara da cewa idan ma da hali suna bukatar Gwamnatin ta samar masu da kamfanonin matse tumatiri ya koma na Gwangwani da kuma kamfanin da zai rika busar da shi ya koma kauda domin manoman kayan gwari da sauran kayan miya su rage yin asarar da suke yi a kowan ne lokaci.
Da fatan Gwamnatin tarayya za ta cigaba da share masu hawayen su a bisa wannan al’ amari, a nasa tsokacin bayan tashi daga taron kusoshin kungiyar na garin Danja Safayanu 0k Danja, kuma wakilin Kungiyar a wajan taron, ya cigaba da cewar a gaskiya wannan taron ya burge shi saboda tun da aka kafa kasuwar mile12 zuwa yanzu bai taba ganin wani shugaban kasuwar ya turo kwamiti zuwa domin jajanta wa manoma kan asarorin da suke yi ba sai wannan lokacin, san nan kuma ya rushe kungiyoyin wadansu tsirarun ‘yan kasuwar da suka takaice mutanen da za su cigaba da kawo kaya a kasuwar domin cin riba su kadai wanda a halin yanzu ya ce ya kashe wannan kowa ya kawo kayan sa a halin yanzu domin saidawa akasuwar ta mile I2 Intanashinal market baki daya da yake cigaba da nasa jawabin bayan tashi daga taron kusoshin kungiyar na garin Danja. Wani daga cikin wakilan kungiyar a wajan taron jajanta wa manoman Arewacin Nijeriya wanda ya gudana a Jihar Kano Sani Sunusi Danja, shi ma ya cigaba da fadin albarkacin bakinsa a game da yadda yake ganin shugaban kasuwar yake kawo gyara tare da kawo abubuwan da za su cigaba da fadada harkokin noman Gwari tare da da kasuwancinta a cikin wadansu jihohin Arewacin kasar nan da Nijeriya baki daya.
ya kara da cewa a madadin ‘yan kasuwar Gwari dake cikin garin Danja yake isar da sakon godiyarsu ga shugaban kasuwar Alhaji shehu usman jibirin samfam, a bisa kokarin da yake yi wa manoma da masu kasuwancin kayan miya na kasar nan domin neman cigaban bangarorin biyu.
Da fatan Allah ya cigaba da yi masa sakayya da Alheri.