Lauyan dan takarar kujerar sanata a shiyyar Kaduna ta tsakiya, Honarabul Usman Ibrahim, wanda aka fi sani da Sardaunan Badarawa da ya fafata a zaben fid da gwani na jam’iyyar PDP da aka kammala, ya bayyana cewa yana rike da hujjojin faifan bidiyo da ke nuna yadda wakilai suka kada kuri’a da arangizon da aka yi a matsayin hujja.
Wani Babban Lauyan Nijeriya (SAN), Samuel Atung ne ya bayyana haka a wata hirar da ya yi da manema labarai a babban kotun tarayya da ke Kaduna.
Lauyan ya bayyana cewa zaben fid da gwanin da ya samar da Lawal Adamu (Mr. LA) a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP na Kaduna ta tsakiya, an tafka kura-kurai da arangizon kuri’u.
Ya kara da cewa wanda yake karewa yana rike da hujjojin faifan bidiyo da na hoton da ke nuna yadda wakilai suka kada kuri’a da ya yi nuni da cewa sun ruguza sakamakon zaben fid da gwani na jam’iyyar PDP.
Ya ce “Bayan jam’iyyar PDP ta Kaduna ta tsakiya ta tsayar da dan takararta na zaben 2023, wanda shi da muke karewa ya rubuta koke ga kwamitin daukaka kara na jam’iyyar yana kalubalantar sakamakon zaben, mun shigar da karar kotu.
“Muna da hujjojin faifan bidiyo a kan haka kuma kwamitin ya yi la’akari da koken da muka yi tare da mika shawararsa ga kwamitin gudanarwa na jam’iyar, wanda a hikimarsa ya bukaci a sake zaben fid da gwani.
“Jam’iyyar PDP ta rubuta wa INEC wasika, inda ta sanar da ‘yan sandan Nijeriya, jami’an tsaron farin kaya da sauran masu ruwa da tsaki kan matakin da ta dauka na sake gudanar da zaben fid da gwani na shiyyar sanatan Kaduna ta tsakiya, wanda abin farin ciki ne, sai kuma ba a yi hakan ba.”
“Abin takaici a ranar da aka saka za a yi zaben, shi wanda muke karewa ya tattaro magoya bayansa zuwa wurin da za a sake zaben fid da gwanin, sai aka ce ba za a sake gudanar da zaben ba saboda yadda jam’iyyar ta tsara kenan.
“Mun zo kotu ne muna neman a tilasta wa jam’iyyar PDP ta mika sunan kowane dan takara domin tabbatar da gaskiya da adalci a zaben 2023 har sai bayan an sake zaben fid da gwanin.
“Muna da kudirin dokar hana PDP mika sunan kowane dan takara ga INEC har sai an sake zaben fid da gwani”, in ji Lauyan.