Kocin Arsenal, Mikel Arteta, ya ce Raheem Sterling yana da wata gudunmawa da zai iya bayarwa ga kungiyar bayan zuwansa aro daga Chelsea.
Dan wasan mai shekaru 29, ya kammala sauya sheka zuwa Arsenal bayan da kocin Blues Enzo Maresca ya bayyana cewar dan Ingilar baya cikin wadanda ya ke bukata a Stamford Bridge.
- Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Murnar Budewar Dandalin Xiangshan Na Beijing Karo Na 11
- Matsalar Tsaro: Sarkin Musulmi Ya Bukaci A Dage Da Addu’o’i
Yanzu dai Sterling na iya buga wasansa na farko a Arsenal a wasan hamayya na arewacin London a ranar Lahadi tsakaninsu da Tottenham, bayan da ya sake haduwa da Arteta wanda ya horar da shi a lokacin da yake Manchester City.
Sterling ya ci wa Chelsea kwallaye 14 a wasanni 59 a gasar Firimiya a kakar wasanni biyu da ya buga na farko, amma Maresca ya ajiye Sterling a benci a wasanni biyu da suka buga a gasar Firimiya ta bana.
“Abin da nake gani shi ne yunwar da ke gare shi na buga wasa, dan wasa ne da ke son yin wasa a kowane minti daya na kowane wasa, idan bai samu haka ba ,ba ya jin dadi,” in ji Arteta.