• English
  • Business News
Sunday, July 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Muna Ganin Kashe-kashe Ta Ko’ina – ‘Yan Gudun Hijirar Sudan

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago
in Kasashen Ketare
0
Muna Ganin Kashe-kashe Ta Ko’ina – ‘Yan Gudun Hijirar Sudan
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Munanan hare-haren da ake kai wa dubun dubatar mazauna sansanin Zamzam ya ci gaba a kwana na uku, kamar yadda mutanen suka shaida wa BBC.

Wani mazaunin sansanin ya ce lamarin ya zama “bala’i”, wani kuma ya ce yanayin “ya ta’azzara”.

  • Fursunoni 62 Sun Rubuta Jarrabawar NECO da MBAIS A Kano
  • Kasar Sin Ta Mallaki Tasoshin Fasahar 5G Miliyan 4.4 A Halin Yanzu

An kashe sama da fararen hula 100, cikinsu har da yara akalla 20 da wata tawagar ma’aikatan lafiya a jerin hare-haren da aka fara kai wa a karshen makon da ya gabata a yankin Darfur, in ji Majalisar Dinkin Duniya (MDD).

An zargi rundunar RSF da kai hare-haren a kan birnin el-Fasher da wasu sansanoni biyu. A ranar Lahadi rundunar ta ce ta karbe iko da sansanin Zamzam amma ta musanta aikata kashe-kashen.

Sansanonin na Zamzam da Abu Shouk wata mafaka ce ga sama da mutum 700,000, da yawansu suna cikin mawuyacin hali na yunwa.

Labarai Masu Nasaba

Iran Ta Zargi Birtaniya, Faransa, Da Jamus Da Gazawa Kan Yarjejeniyar Nukiliyar 2015

Bayan Shekaru 20 Yana Bacci, Yariman Saudiyya Ya Rasu

Labarin harin na zuwa ne kwana daya kafin cika shekara biyu da fara yakin basasar na Sudan tsakanin RSF da rundunar sojin kasar.

Da yake magana da BBC a safiyar Lahadi, wani mazaunin Zamzam da ke aiki da wata cibiyar da ke tallafa wa mutane da abinci ya ce an kashe “matasa da yawa”.

“An kashe masu aiki a cibiyar, haka ma an kashe likitocin da ke aikin kula da lafiya a cibiyar,” a cewar Mustafa mai shekara 34 cikin wani sakon murya ta WhatsApp.

“An kashe kawuna da dan dan’uwana. An raunata mutane kuma babu magani ko asibitin da zai kula da su – suna mutuwa saboda zubar jini.

“Har yanzu ana ci gaba kawo hari, kuma muna tunanin za a ci gaba da yin hakan har zuwa safiya.”

Ya kara da cewa an rufe dukkan hanyoyin fita daga sansanin “kuma dakaru sun zagaye duka bangarori hudu”.

Wani mutum mai suna Wasir ya ce “babu komai da ya rage a Zamzam”.

“Fararen hula masu yawa sun gudu, mu ma muna kokarin tafiya amma ba mu yi nasara ba, an rufe duka titunan, ga kuma yara a tare da mu.

Mutuwa ta ko’ina. Yanzu da nake magana da ku daga cikin wani rami, ana ta luguden wuta.”

Wasu daga cikin mazauna sansanin sun samu tserewa kuma suka yi tafiyar kilomita kamar 15 zuwa el-Fasher, a cewar Ministan Lafiya na Arewacin Darfur Ibrahim Khater.

“Na ga mutane da yawa suna barin Zamzam da kafa – akasarinsu yara, da mata, da tsofaffi,” in ji shi.

“An raunata wasu, wasu agajiye bayan an kashe ‘yan’uwansu. Lamarin ya ta’azzara.”

Jagorar tattara kayan agaji na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan, Clementine Nkweta-Salami, ta ce “ta kadu sosai” da jin rahotonnin da ke fitowa daga Darfur.

“Wannan na nuna irin yadda ake tsananta hare-haren rashin imani kan mutanen da aka kora daga muhallansu da masu aikin agaji,” a cewarta cikin wata sanarwa.

Ita ma ma’aikatar harkokin Amurka ta yi “tir da rahotonnin hare-haren da RSF ta kai a Zamzam da kuma Abu Shouk”, tana cewa: “Muna yin Allah wadai da hare-haren RSF kan fararen hula marasa karfi.”

Kungiyar bayar da agaji ta Relief Organization ta ce ma’aikatanta tara “aka yi wa kisan rashin imani cikinsu har da likitoci, da direbobi, da wani jagoran tawaga” a harin da aka kai a Zamzam.

Kungiyar, wadda ta ce ita kadai ta rage da ke aikin kula da lafiya a sansanin, ta zargi RSF da aikata laifukan.

“Mun fahimci cewa wadannan hare-hare ne da gangan kan cibiyoyin lafiya a yankin domin hana ‘yan gudun hijira samun magani.

“Muna cikin zulumi ganin yadda aka hari daya daga cikin cibiyarmu da sauran cibiyoyin lafiya a el-Fasher.”

Kashif Shafikue, shugaban kungiyar, ya fada wa BBC cewa abin da ya faru da gangan aka aikata shi.

Kamar yadda wata ma’aikaciyar lafiya da ta tsira ta bayyana masa, ya ce mayakan RSF sun shiga wata maboyar mutane suka harbe mutum tara a ka da kuma kirjinsu.

CIkin wata sanarwa a ranar Asabar, RSF ta ce ba ita ce ta kai hare-hare kan fararen hular ba, kuma wai an shirya hare-haren ne domin a shafa mata kashin kaji.

Kwana daya bayan haka ne kuma ta ce “ta yi nasarar ‘yanta” sansanin daga hannun dakarun Sudan.

RSF ta zargi sojojin kasar da yin amfani da Zamzam “a matsayin sansanonin soji da kuma fararen hula a matsayin garkuwa”.

Wata tawagar kwararru a jami’ar Yale da ke Amurka ta ce hotunan tauraron dan’Adam da ta nazarta sun nuna “harin ya zama mafi muni da aka kai ta kasa a kan Zamzam…tun bayan fara yakin a el-Fasher cikin shekarar 2024”.

Ta ce ta lura da yadda “hare-haren amfani da wuta suka kona gine-gine da wurare da yawa a tsakiya, da kudanci, da kudu maso gabashin sansanin”.

Yakin da ake yi domin kwatar iko tsakanin RSF da sojin gwamnatin Sudan, ya jawo bala’i mafi girma a duniya a kan al’umma, inda ya tilasta wa sama da mutum miliyan 12 barin gudajensu da kuma jefa su cikin yunwa.

An fara gwabzawa a ranar 15 ga watan Afrilun 2023 bayan shugaban RSF da shugaban Sudan sun samu sabani game da makomar kasar.

El-Fasher ne gari mafi girma a yankin Darfur da ke karkashin ikon sojoji, wanda RSF suka kewaye tsawon shekara daya.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Gudun hijiraSudan
ShareTweetSendShare
Previous Post

Tsarin BRICS Ya Zama Muhimmin Dandalin Hadin Kai Na Kasashe Masu Tasowa

Next Post

Baje Kolin Kayayyakin Masarufi Na Duniya Ya Kara Fito Da Kyawun Kasuwar Sin

Related

Iran Ta Zargi Birtaniya, Faransa, Da Jamus Da Gazawa Kan Yarjejeniyar Nukiliyar 2015
Kasashen Ketare

Iran Ta Zargi Birtaniya, Faransa, Da Jamus Da Gazawa Kan Yarjejeniyar Nukiliyar 2015

6 days ago
Bayan Shekaru 20 Yana Bacci, Yariman Saudiyya Ya Rasu
Kasashen Ketare

Bayan Shekaru 20 Yana Bacci, Yariman Saudiyya Ya Rasu

1 week ago
Trump Ya Bai Wa Rasha Kwanaki 50 Ta Kawo Ƙarshen Yaƙinta Da Ukraine
Kasashen Ketare

Trump Ya Bai Wa Rasha Kwanaki 50 Ta Kawo Ƙarshen Yaƙinta Da Ukraine

2 weeks ago
Sarkin Maroko Ya Aike Da Ta’aziyya Ga Nijeriya Bisa Rasuwar Buhari
Kasashen Ketare

Sarkin Maroko Ya Aike Da Ta’aziyya Ga Nijeriya Bisa Rasuwar Buhari

2 weeks ago
Aikin Bututun Gas Na Nijeriya – Morocco Na Ƙara Samun Ci Gaba
Kasashen Ketare

Aikin Bututun Gas Na Nijeriya – Morocco Na Ƙara Samun Ci Gaba

2 weeks ago
Cote d’Iboire Ta Amince Da Kafa Bankin Makamashi Na Afirka
Kasashen Ketare

Cote d’Iboire Ta Amince Da Kafa Bankin Makamashi Na Afirka

2 weeks ago
Next Post
Baje Kolin Kayayyakin Masarufi Na Duniya Ya Kara Fito Da Kyawun Kasuwar Sin

Baje Kolin Kayayyakin Masarufi Na Duniya Ya Kara Fito Da Kyawun Kasuwar Sin

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Ta Ba Da Wa’adin Mako 6 Don Kammala Ginin Rukunin Gidaje A Kano

Gwamnati Ta Ba Da Wa’adin Mako 6 Don Kammala Ginin Rukunin Gidaje A Kano

July 27, 2025
Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu

Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu

July 27, 2025
ADC Ce Za Ta Haɗa Kan Arewa Wajen Kawo Ci Gaba — Mark

ADC Ce Za Ta Haɗa Kan Arewa Wajen Kawo Ci Gaba — Mark

July 27, 2025
Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

July 27, 2025
Ƴansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 6 A Kaduna Da Zamfara

Ƴansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 6 A Kaduna Da Zamfara

July 27, 2025
aure

Ko Kin San… Matsalolin Mahaifa Da Suke Hana Haihuwa 

July 27, 2025
VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace

VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace

July 27, 2025
Yadda Ake Faten Acca

Yadda Ake Faten Acca

July 27, 2025
Hanyoyin Gyaran Gashi

Hanyoyin Gyaran Gashi

July 27, 2025
Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

July 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.