• English
  • Business News
Wednesday, October 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Muna Gyara Da Gina Sabbin Makarantu 290 A Zamfara – Gwamna Dauda

by Leadership Hausa
1 year ago
makarantu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa suna gyara tare da gina wasu sabbin makarantu 290 a fadin jihar domin bunkasa ilimi.

Gwamnan ya kuma bayyana Kwalejin Ilimi ta Tarayya ta ƙere-ƙere da ke jihar a matsayin wani ginshiƙin samar da ƙwararrun malamai a makarantun gwamnati a Zamfara.

Majalisar Gudanarwa ta Kwalejin Ƙere-ƙere ta Tarayya (Technical) da ke Gusau, ta kai wa Gwamna Lawal ziyarar ban-girma a gidan gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau a ranar Laraba.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, sun kai ziyarar ban-girma ne domin fahimtar juna da kuma inganta haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da majalisar FCET ta Gusau.

makarantu

LABARAI MASU NASABA

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya yi maraba da mambobin majalisar gudanarwar tare da jaddada buƙatar bai wa Kwalejin Ilimi ta Tarayya duk kulawar da ta dace.

“Ina so in fara da cewa al’ummar Jihar Zamfara sun daɗe suna cin gajiyar Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Gusau. In ma taƙaice zance: ‘yan uwana mata kusan biyar ne suka yi karatu a FCET.

“Kamar yadda shugaban ya bayyana, a fannin ilimi, Jihar Zamfara ta kasance a baya tsawon shekaru. Gogayya muke yi da Yobe a matsayi na ƙarshe.

“A shekarar da ta gabata, na kafa dokar ta-ɓaci a ɓangaren ilimi na Zamfara saboda ƙalubalen da ake fuskanta a fannin. Abin takaici, a cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnatin da ta shuɗe ta kasa biyan kuɗin jarrabawar NECO da WAEC na ɗalibai. Duk da haka, mun biya bashin, wanda yanzu ya zama tarihi.

“Kwanan nan, mai yiwuwa ka karanta a labarai game da ƙwazon da ɗalibanmu suka yi a jarrabawar ɗalibai masu hazaƙa na NECO. Jiharmu ta Zamfara ta zama jihar da ta yi zarra a duk faɗin Arewa kuma ta biyu a faɗin ƙasar nan.

“Mun himmatu wajen ganin kowane yaro ya samu ingantaccen ilimi. A yanzu haka muna gyara da gina makarantu sama da 290 a faɗin jihar nan.

“Matakan da muke ɗauka sun haɗa da samar da ingantattun kayan karatu da kuma ba da horo ga malaman mu. A cikin wannan yunƙurin, FCET tana taka rawar gani yayin da muke son haɓaka iyawa da ingancin malaman mu. Don haka za mu yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa domin gyara harkar ilimi a Jihar Zamfara.

Tun da farko, Farfesa Muhammad Bashir Nuhu, shugaban majalisar gudanarwa na Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Technical), ya yaba wa gwamnan bisa ba da fifiko ga ilimi a cikin ajandar gwamnatinsa.

makarantu

Ya ce, “Mu ne majalisar gudanarwar babbar kwalejin FCET. Ana ɗaukarta da daraja domin ita kaɗai ce irinta a faɗin tarayyar ƙasar a lokacin da aka kafa ta. Lokacin da aka kafa ta, an yi ta hassada da yawa game da dalilin da ya sa aka kafa ta a Zamfara. Daga baya na gane cewa wannan ya faru ne saboda jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar ilimi.

“A yau, mun zo nan ne saboda gwamnatin ku ta ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi na jihar da kuma kyawawan matakan da kuke ɗauka na inganta fannin.

“Muna yaba muku da ƙoƙarinku, kuma muna so mu yi amfani da wannan dama wajen yaba wa uwargidan gwamna Hajiya Huriyya Dauda, ​​wadda ta ɗauki nauyin ɗalibai 20 a ƙwalejin tare da bai wa ɗalibai uku na farko da suka yaye na’ura mai kwakwalwa guda uku.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

gombe
Ilimi

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma
Ilimi

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
ASUU
Ilimi

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Next Post
Sin Ta Harba Gungun Taurarin Dan Adam Na Binciken Doron Kasa

Sin Ta Harba Gungun Taurarin Dan Adam Na Binciken Doron Kasa

LABARAI MASU NASABA

Nesa Ta Zo Kusa: Maraba Da Sabon Jirgin Kasa Samfurin CR450 Da Kasar Sin Ta Kera

Nesa Ta Zo Kusa: Maraba Da Sabon Jirgin Kasa Samfurin CR450 Da Kasar Sin Ta Kera

October 22, 2025
An Sake Saka Sunan Osimhen A Cikin ‘Yan Takarar Kyautar Gwarzon Dan Wasan CAF Na Bana

An Sake Saka Sunan Osimhen A Cikin ‘Yan Takarar Kyautar Gwarzon Dan Wasan CAF Na Bana

October 22, 2025
Adadin Yawon Shakatawa Da Mutanen Sin Suka Yi A Cikin Gida Ya Zarce Biliyan 4.998 Tsakanin Janairu Da Satumban Bana

Adadin Yawon Shakatawa Da Mutanen Sin Suka Yi A Cikin Gida Ya Zarce Biliyan 4.998 Tsakanin Janairu Da Satumban Bana

October 22, 2025
Tinubu Ya Amince Da Tallafin Naira 250,000 Ga Ƙananan ’Yan Kasuwa A Jihar Katsina

Tinubu Ya Amince Da Tallafin Naira 250,000 Ga Ƙananan ’Yan Kasuwa A Jihar Katsina

October 22, 2025
Kasar Sin Ta Sake Farfado Da Muhimman Koguna Da Tafkuna 88 A Kokarin Inganta Muhalli

Kasar Sin Ta Sake Farfado Da Muhimman Koguna Da Tafkuna 88 A Kokarin Inganta Muhalli

October 22, 2025
Tanka

Majalisa Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kai Agajin Gaggawa Ga Waɗanda Fashewar Tanka Ta Shafa A Neja

October 22, 2025
Zimbabwe Ta Jinjinawa Jarin Sin A Matsayin Wanda Ya Bunkasa Masana’atun Samar Da Siminti A Kasar

Zimbabwe Ta Jinjinawa Jarin Sin A Matsayin Wanda Ya Bunkasa Masana’atun Samar Da Siminti A Kasar

October 22, 2025
Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki 

Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki 

October 22, 2025
Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi

Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi

October 22, 2025
Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal

October 22, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.