Umar A Hunkuyi" />

Muna Karfafa Wa Sojoji Gwiwa Ta Hanyar Dadada Musu –Rundunar Soja

Rundunar Sojin kasar nan tana karfafa gwiwar dakarunta ta hanyar dubarun yi masu sakamako da alherai musamman wadanda suke fafatawa a yakin da ake yi da ‘yan ta’addan Boko Haram.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Sani Usman, ne ya bayyana hakan, sa’ilin da yake amsa tambaya ga majiyarmu, a Abuja, ranar Juma’a.
Ya bayyana cewa, rundunar a karkashin jagorancin Laftana Janar Tukur Buratai, suna nuna bajinta da jarunta a aikin da suke na sauke nauyin da tsarin mulkin kasar nan ya dora masu na kare kasar nan daga duk wata barazana a ciki ko daga wajen kasar nan.
Usman ya ce, “Ana yin abubuwa masu yawa domin karfafa gwiwar dakarun a duk lokacin da aka tura su fagen fama. Na farko dai ana ba su horon da ya kamata. Muna tabbatar da cewa, Sojojinmu sun sami duk horon da ya dace, suna kuma ci gaba da samun horon.
“Na biyu, duk wasu kudade da alawus-alawus din su ana biyansu. Na Uku, shi ne maganan kayan aiki da kayan jin dadin su da kuma shugabanci nagari.
“Daga su kansu dakarun da suke a fagen daga, da iyalansu da suka bari a gida, duk kula da lafiyarsu yana da matukar mahimmanci, har wajen kasar nan mukan kaisu domin duba lafiyarsu in bukatar hakan ta taso.”
Usman ya kara da cewa, “Akwai kuma sauran tallafi da alawus kamar na daukan nauyin duk dawainiyar rufe matattun su, kudaden inshora na jin dadin Sojoji, biyan kudaden mutuwa da kudaden Inshoran rai, duk da ake biyan su.
“Hakanan, rundunar Sojin takan dauki nauyin ilimin yara hudu na matattun dakarun namu, tun daga karatun su na Firamare har ya zuwa karatun su a manyan makarantu. Akwai kuma kokarin da ake yi na inganta wuraren zaman su a cikin barikokin su.”
Usman ya kara da cewa, “A sa’ilin da dakarunmu na bataliya ta uku ta, Operation Lafiya Dole, suka yi biji-biji da ‘yan ta’addan Boko Haram, da suka yi yunkurin shiga inda suke a Monguno, an biya su ribanyin kudaden alawus din da ake biyan su a duk wata.”
Sai dai, ya karyata rade-radin da wasu ke yi na cewa, Sojoji suna da hannu a binciken zargin da ake yi wa wasu ‘yan siyasa na safarar bindigogi da albarusai zuwa cikin kasar nan domin zaben 2019.
Rundunar Sojin kuma ta yi roko ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da ba ta goyon baya wajen kare kasar nan.

Exit mobile version