Muna Kashe Naira Biliyan 30 Duk Wata A Shirin N-Power – Gwamnatin Tarayya  

N-Power

Daga Yusuf Shuaibu,

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa a duk wata tana kashe naira biliyan 30 kan wadanda suke ci moriyar shirin N-Powar.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne ta bakin Ministar Jinkai, Sadiya Umar Farouk a wurin rufe taron koyar da wadanda suka ci moriyar shirin N-Power guda 3,000 sana’o’in hannu da injiniyar manhajan kwamfuta karkashin tsarin N-Tech wanda ya gudana a Abuja.

Ministar wacce ta samu wakilcin Ko-odineta na shirin bunkasa zuba jari ta kasa, (NSIP), Dakta Umar Bindr, ta bayyana cewa sama da ‘yan Nijeriya miliyan daya ne suke ci gajiyar shirin N-Power a duk shekara wanda ya kara taima wa shirin da Shugaban Kasa Muhummadu Buhari ya bullo da shi na cire ‘yan Nijeriya miliyan daya daga kangin talauci.

“Idan ana samu matasa da suka kammala karatu guda miliyan daya ciki shirin NSIP a duk wata har na tsawan shekara guda wanda ake biyansu naira 30,000, kowani wata ana kashe naira biliyan 30 wajern biyan wadanda suka ci moriyar shirin, sannan idan aka lissafa a shekara za a samu jimmillar kudi na naira biliyan 360.

Wadanda ba su kammala karatunsu ba suna da nasu bangaran wanda kunshi kwamfuta da sauran kayayyaki, ana ba su horo ta yadda daga baya za su fara gudanar da harkokin kasuwancinsu.

“A duk shekara gwamnati tana zuba jari wanda ya kai kimanin naira biliyan 300 zuwa 400 a kan wannaan shiri. Shirin NSIP yana daya daga cikin muhimman shirye-shiryen kawar da talauci a Nahiyar Afirka,” in ji ta.

Ministar ta bukaci wadanda suka ci moriyar shiri da su yi amfani da basirar da suka koya wajen ci gaba al’umma.

 

Exit mobile version