Farfesa Khalifa Dikwa, Shehin Malami ne a Jami’ar Maiduguri, Tsangayar Koyar da Ilimin Harsuna da Alakar Kasa-da-Kasa (Sociolinguistics, International Relations), a tattaunawarsa da LEADERSHIP Hausa, ya warware zare da abawa kan munakisar turawan yamma a Afirka da alakar hakan da juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar. Wakilinmu, Muhammad Maitela ya yi tattaunawar kamar haka:
Duk da ci gaban da duniya ta samu, me ya sa har yanzu ake yawan samun juyin mulki a Kasashen Afrika?
Da farko dai, ko shakka babu yanzu mutanenmu sun fara wayewa dalilin samuwar wasu kafafen watsa labaru (Social Media), sabanin talakawan manyan kasashen duniya; wadanda ba su san abubuwan da gwamnatocinsu ke aikatawa ba. Saboda haka, wannan juyin mulkin ana tsammanin sa domin yana kan hanya ne, sakamakon yadda talakawan kasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka suka nuna cewa abin ya ishe su haka nan.
Dalili kuwa ga su da arzikin amma suna fama da bakin talauci, sannan dukkan arzikin da yake karkashin kasa, a kasashen da ta yi wa mulkin mallaka a Afrika, Faransa ce ke kwashe su dari bisa dari. Kazalika, duk abin da za a yi na horas da sojoji da sauran jami’an tsaro duk Faransa ce kadai ke aiwatar da su, amma wata kasa ba ta da wani iko hatta a kan duk ma’adanan da suke karkashin kasa; wannan tun bayan samun ‘yancin kai na ranar 3 ga watan Agustan 1960.
Bugu da kari, bayanan da Shugaban Kasa Mohammed Bazoum ya yi na cewa, dole gwamnatinsa ta yi kokarin kwato kasar daga halin kangin da Nijar take ciki, musamman na bakin mulkin Faransa tare da nuna kudin SAIFA na tunatar musu da cewa, kamar har yanzu suna cikin kangin bauta ne. Don haka, sun fi yarda su kasance tare da Nijeriya, musamman ganin kasancewar ta a matsayin makociyarsu, shakka babu wannan na daya daga cikin abin da ya jawo wannan halin da ake ciki yanzu.
Dauki misali, kwanan baya Kasar Mali ta kori Sojojin Faransa daga kasarta, amma maimakon su koma kasarsu, karfi da yaji sai suka koma Nijar. Haka nan, a koda-yaushe idanun Faransa na Nijeriya, tun kuwa lokacin yakin Basasan Nijeriyar, ba su daina kulla makirce-makirce ba, wanda hatta sunan Biafra ya samo asali ne daga kalmar ‘Bia’ Inyamuranci (zo) ‘Fra’ ma’anarta France. Kowane lokaci burinta tayar wa da Nijeriya da hankali ta yin amfani da kasashen da ta yi wa Mulkin Mallaka a Afrika.
Wanda hatta kasafin kudaden wadannan kasashen, ba zai aiwatu ba har sai sun samu izini daga Ministan Kudin Faransa, sannan kuma dukkan arzikin da suka mallaka 85 cikin dari, na cikin Bankunan Faransa (France Treasury), za a ba su kaso 15 ne kacal cikin dari na ayyukan kwangila, idan kuma ba su yarda da ayyukan ba su ki yarda.
Haka zalika, idan wadannan kudade ba su ishe su ba, dole sai sun yi roko don a ba su bashi mai ruwan gaske. Sannan kuma, kasar ta Faransa ce take buga wa kasashen da ta yi wa mulkin mallaka kudin da hatta a Faransar ba zai yi wa amfani ba. Kazalika kuma kasar Faransar ba za ta yarda kasar da ta yi wa mulkin mallaka ta yi mu’amala da wata kasa daban ba, musamman ma Nijeriya.
Har wa yau kuma, duk wani Shugaba a Nijar da ya tsaya ya jajirce wajen ganin cewa an ba su wani kaso daga cikin ma’adanan dukiyar kasar da sauran makamantan su, juyin mulki ne zai biyo bayansa. A shekarar 1974 lokacin Hamani Jori ya bayyana cewa suna so a bai wa kasarsu kason tattakin arzikin kasar, daga nan juyin mulki ne ya biyo baya. Haka nan abin yake a sauran Kasashen Afrika wadanda Faransa ta yi wa mulkin mallaka, ba su tsira daga makircinsu ba. Sannan kuma, hatta kasashe renon Ingila ma ba su tsira ba, hakan ne ya rutsa da tsohon Shugaban Kasar Chadi Mista Tambalbay, inda sojojinsa suka hallaka shi.
Har ila yau, an sha zargin Kasar ta Faransa da hannu a cikin kashe-kashen shugabannin da ake yi a Kasashen Afrika, motsi kadan sai ka ji an yi juyin mulki, idan sun bayyana burinsu na ganin an kyautata wa rayuwar al’ammar kasashensu. Sannan duk da irin maganganun da kasashen Italiya ke yi na mutuwar matasa ‘yan-ci-rani cikin Teku wajen tsallakawa zuwa Turai, cewa suke yi muddin Faransa ba ta daina wadannan abubuwan da take yi ba a Kasashen Afrika, ba za a kawo karshen mace-mace ba amma ko kadan wannan bai dame ta ba.
Sannan makamashin Yuraniyom da ake tonowa a Nijar, kimanin kaso 40 cikin dari Faransa ce ke amfani da shi wajen samar da wutar lantarki a masana’antunta da sauran makamantan su, daga Nijar take hako su, wanda zai yi wuya ka samu kaso 20 cikin dari na talakawan Nijar wadanda ke iya samun hasken wutar lantarki.
Wani zai iya cewa mene ne sahihancin wadannan bayanai masu sarkakiya haka?
To, bisa hakikanin gaskiya muna samun wadannan bayanan ne ta hanyar nazarce-nazarce, sannan kuma bisa ga zahiri ina zuwa har Faransa na gudanar wa da dalibaina lakca, sannan kuma na kan fada wa daliban nawa irin abubuwan da gwamnatocin suke yi a kasashen waje. Kamar talakawan Amurka ne ba su san abin da ke wakana a Afrika ba kwata-kwata; eh, ba su da ilimin halin da kasashen duniya suke ciki, da za ka tambayi talakan Faransa ko Amurka, ina Nijar ko Afrika take? ba su sani ba. Sabanin yaranmu, sun san ina Kasashen Turai suke, saboda yadda suka samu ilmi daban-daban tun suna kanana.
Suna so a yi juyin mulkin da kasar Faransa ke so, amma su kuma Kungiyar Kasashen Turai, za ka samu cewa kullum sai faman yada karairayi da farfaganda suke yi tare da nuna wariyar launin fata, suna kwaikwayon abin da kasar Amurka ke yi, babu kunya ba tsoron Allah, musamman guntuwar matar nan; Sakatariyar Kungiyar Tarayyar Turai, Ursula Gertrud Bon Der Leyen, ba ta jin kunyar yin karya. Kowane lokaci bukatarsu ita ce dole a biya musu burin kasashensu, idan Shugabanin Kasashen Afrika suka ki sai su yi amfani da wasu hanyoyi wajen kifar da gwamnatocinsu. Kuma dole Shugabanin Kasashen Afrika su ba su dama, domin su ci gaba da wawushe albarkatun da Allah ya azurta su da su, ba tare da damuwa da talaucin da ya yi musu katutu ba.
Yanzu dauki misalin bai wa ‘yan kasa tallafin abubuwan more rayuwar yau da kullum na al’umma, Kasashen Turai suna bai wa al’ummar kasashensu tallafi na kimanin kaso 80 cikin dari na man fetur, hasken wutar lantarki da gas; sabanin kasashenmu na Afrika. Dukkan abubuwan da suke yi don inganta rayuwar al’ummarsu ne, akasinsa kuwa shi ne suke tilasta wa Shugabannin Kasashen Afrika su janye tare da yi wa shugabanin barazanar idan ba su yi ba, za su tona asirinsu da yake a hannunsu: “Idan ba ku yi abin da muke so ba, za mu fallasa ku, kuma mu sa kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ta daure ku.” Da wannan barazanar suke bai wa gwamnatocinmu tsoro.
Har wa yau kuma, wadannan manyan kasashe na duniya ba sa kaunar hulda da wanda bai taba yin wata barna ya zama Shugaba a Afrika ba. Kullum suna son mutum mai laifi ko mai rauni sannan kuma ya zama matsoraci. Haka nan, a fannin ilimi ma suna iya kokari wajen ganin al’amuran ilimi sun tabarbare a cikin wadannan kasashe na Afrika, wanda kamata ya yi a ce duk dan kasa ya samu ilmi mai inganci, kama daga matakin farko zuwa na Jami’a, amma sun hana kuma sun dakile samar da ilmin da zai yi wa kasashen amfani. Amma a Jamus ko Faransa, suna sa a dauki nauyin yaranmu don su samu ilmin yadda za a sarrafa albarkatun da muke da su na man fetur da zinariya a Afrika kamar a Jihar Zamfara.
Haka nan, za ka samu wanda cewa kungurmin jahili ne wanda bai san komai ba, Turawa sun turo shi Afrika, sannan ka ga mutanenmu na girmama shi. Amma a nan Nijeriya wani gwamna zai iya wulakanta ka, har ta kai ga ana iya korar ka daga aiki ko a gida, alhali su kuma suna dibar masu ilminsu suna kai su kasashensu, har ma su ba su izinin zama dan kasa don girmama ilmin nasu. Sannan kuma, suna yin duk yadda za su iya wajen hana ruwa gudu ta fannin samun ci gaban kasa, misali a Nijeriya kamar matsalar wutar lantarki da gyara matatun man fetur duk su ne suke hanawa. Dubi Kamfanin Karafa na Ajakuta, an kammala sama da kaso 90 cikin dari, amma suka tilasta Nijeriya dole sai ta rusa shi.
Farfesa, sojoji sun yi juyin mulki a Nijar, shin wadanne kasashe ne ke kan gaba wajen rura wutar rikicin da ke son rikidewa zuwa yaki?
Abin da ya kamata jama’a su sani shi ne, Rasha da ake jin tana tsoma baki, ita kamar Chana ce duk yarjejeniyar da kuka sanya hannu a kai da ita haka za a yi, sabanin Turawa ko kuma Kasar Amurika, dukkan alkawarin da kuka yi da su cikin 10 ko daya ba za su cika ba; nan take za su bijire. Kuma idan dai kai malalacin shugaba ne, Amurka da kawayenta za su ba ka kowace irin dama ka saci kudi ka je can kasashensu ka boye tare da gine-gine a wajen nasu, amma Rasha duk sharadin da kuka yi da ita na Sojan Wagner, suna nan a kasashen duniya daban-daban, kuma suna gudanar da ayyuakansu da gaske.
Amma a nan ga sojojin Faransa jibge, amma ba zai hana ‘yan ta’adda su yi barnar da suke son yi ba. Idan ka tuna Ruwanda, Sojoji Faransa suna gani aka yi wa sama da mutum miliyan biyar kisan kiyashi a kasar, al’amarin da ya fusata Shugaban Ruwandan ya sauya harshen Faransa da na Turanci. Sannan kuma, Kasashen Faransa da Amurka suna rige-rige wajen gasar samun gindin zama a Nahiyar Afrika, saboda ma’adanai da albarkatun kasa. Sakamakon haka, duk inda ka ga ana tashin hankali a Afrika; idan ka bincika akwai ma’adanai a wajen, kuma dukkan wadannan fitintinun, yawaitar muggan makamai da miyagun kwayoyi da ke yawo a wannan Nahiya tamu ne suke kera su tare da raba su ga mutane, musamman ta hannun kungiyoyin leken asiri na Amurka, Ingila da Isra’ila su ne ke kitsa rigingimun addini da na kabilanci don a samu rikici.
Wannan dalili ne ya sa ba sa son Rasha ta zo tana taimakawa kai-tsaye, alhali su kuma a nasu tsarin babu maganar taimako. Yayin da hatta inganta tsarin ilmi sun hana, domin sun san idan yaro ya tashi ya san cewa gwamnati ce ta tallafa masa ya samu ilmi mai inganci da sauran makamantan su, zai sa ya tashi da kishin kasa, amma idan aka sanya komai sai mahaifinsa ya biya, ko albashi ba ya isar ma’aikaci (duk su ne suke tsarawa ta bayan fage). Haka nan ka bincika batun dukkanin kungiyoyin ‘Yan Ta’addan Boko Haram, Al-ka’ida da Al-Shabab da sunaye daban-daban. Saboda haka, wannan juyin mulki da aka yi a Nijar yanzu, akwai yiwuwar sauran kasashen Afrika ma su biyo sawu. Domin kowa ya gaji da bakin mulkin Faransa, sannan ita kuma girman kai ya hana ta saduda ta dawo daga wannan danniya da take yi wa kasashen da ta rena.
Kowane lokaci tunaninta shi ne, za a ci gaba da bautar da wadannan kasashe; sai abin da take so shi za a yi, amma ko shakka babu idan ba a yi hankali ba, talakawa za su yi boren neman sojoji su yi juyin mulki. Kuma idan abin ya ci gaba, nan gaba talakawa da kansu za su kwace kasashensu da kansu, sakamakon yadda tsananin talauci ke dada kamarin da zai kai talaka bango, ko za a kashe su ba za su saurari kowa ba. Sannan idan matsalar juyin mulkin sojoji ne, to ina maganar wasu Shugabanni a Afrika wadanda suka sauya dokokin kasa don samun gindin zama? Irin su Alasan Watara na Kwadibuwa, wanda ya canja kundin tsarin mulki don zarcewa kan karagar mulkin. Ina zancen Alfa Kwande na Gini-Bisau, shi ma ya canja kundin tsarin mulki ya zauna, kafin sojoji su karbe.
Idan ka leka kasar Senigal, mutumin da yake da farin jinin jama’a, Usman Zanko, sai da aka tuhume shi da laifin da bai aikata ba don kawai a hana shi tsayawa takarar shugaban kasa shekara mai zuwa, wanda muddin bukatar Faransa za ta biya an gama magana. Dalili kuwa, mun gani a Kamaru, tun 1982 Faransa ta ture Ahmadu Ahijo saboda yana da alaka da Nijeriya aka nada Paulbia, yau kimanin shekara 41 yana mulki a Kamaru, kuma duk da yawan shekaru da rashin lafiya; amma haka ya ci gaba da shugabancin kasar. Hakan ya taba faruwa a Gabon, inda Umar Bango ya yi ta mulki har dansa ya gaje shi a mulkin; Faransa ta mika musu rakumi da akalar kasar, don tana samun duk abin da take so.
Sannan ya dace ‘Yan Nijeriya su san cewa, rusa Kasar Libiya ne ya jawo ruruwar ta’addancin da ya mamaye Kasashen Afrika, kuma hakan ya zo ne sakamakon yunkurin da Shugaba Mu’ammar Gaddafi ya yi na cewa, dole Afrika ta samu kudin bai-daya, kuma a samu banki daya tare da bayar da kaso 90 cikin dari na kudin da za a kashe, kuma shalkwatar Bankin ta zama a Kamaru. A kan wannan manufa ne suka taru suka rusa Libiya, kasar da take da kudade ajiye a bankuna daban-daban, wadda kuma ta kasance tamkar aljanna ga ‘yan kasarta. Amma an wayi gari wadannan manyan kasashen duk sun tarwatsa ta filla-filla, yanzu babu tsayayyar gwamnati mai cikakken iko ta bai-daya a Libiya. Bugu da kari kuma, duk sun sace wadannan kudade, babu kuma mai iya tambayar wane ne ya wawushe su, face kawai Faransa da kawayenta wadanda ke cin karensu babu babbaka.