Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NAZARI

Muryar Talaka: Tsakanin Masu Son Ruguzawa Da Masu Son Sauya Fasalin Ƙasa (II)

by Tayo Adelaja
October 11, 2017
in NAZARI
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tare da Bishir Dauda 08165270879

Ranar Litinin 25 ga watan Satumbar 2017, jihohi uku daga cikin bakwai na Arewa Maso Yamma suka gudanar da sauraren ba’asi kan sauya fasalin Nijeriya.  Jihohin sun haɗa da Kebbi, Sokoto da Zamfara. Kuma an gudanar da wannan taro ne a babban ɗakin taro na kwalejin marigayi sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo, da ke Birnin Sokoto.

samndaads

Gwamnonin Sokoto, Kebbi da kuma muƙ addashin gwamnan Jihar Zamfara, Mallam Muhammad Ibrahim Wakkala, suna a wurin wannan taro.

Sannan taron ya samu halartar ƙ ungiyoyin farar hula daga jihohin. Wannan taro dai kamar yadda na faɗa a baya, jam’iyya mai mulkin ƙ asar nan ce, wato APC ta shirya shi, domin tattara bayanai kan ra’ayin ‘yan Nijeriya akan abin da ya shafi maganar da a ke ta yamadidi akan ta,ta sauya ma Nijeriya fasali. Jam’iyyar ta APC ta kafa kwamitin da ta kira “kwamiti kan tsarin tarayya na gaskiya” Abin da muka tattara dangane da ra’ayin da aka bayyana wajen wannan taro shi ne, ba a goyi bayan  duk wani sauya fasali da zai nakasa ƙ asar Nijeriya ba ko ya maishe da gwamnatin tsakiya ta jeka-na-yi-ka ba.

Nan ma, baƙ i ya zo ɗaya, domin gwamnatocin, musamman Katsina da Kano sun fito  ɓ alo- ɓ alo, sun yi watsi da batun rage wa gwamnatin tsakiya ƙ arfi. A ta baƙ in gwamnan Jihar Kano, wanda yai magana a madadin Jiharsa “Muna goyon bayan dunƙ ulalliyar tarayyar Nijeriya, wadda gwamnatin tsakiya ke da ƙ arfi.” Shi ma takwaransa daga Jihar Katsina, Aminu Bello Masari cewa yayi “Katsina, Kano da ɗaukacin jihohin Arewa maso Yamma naɗa addini, al’ada da muradi iri ɗaya, don haka abin da duk ya shafi ɗaya daga cikin waɗannan jihohi, to ya shafi ɗaukacin yankin” Ya kuma nuna buƙ atar a samu Nijeriya wadda ke da gwamnatin tsakiya mai ƙ arfi. Amma duk da haka, ya bayyana cewa bai kamata a ce kuma wasu ayyukan gwamnatin tarayya ke yin su ba. Misalin da ya bada shi ne batun albashi na bai ɗaya.

Kodayake, yawancin ƙ ungiyoyin da suka halarci wannan taro basu tsawaita magana ba, to amma daga gabatarwar da suka yi ya nuna, kowa yasan inda aka dosa, kuma mutanen Arewacin ƙ asar nan, sun fahimci tarkon da mutanen kudu suka dana masu.

Kada mu manta da yawa daga cikin batutuwan da a ke magana akai ƙ arƙ ashin sauya fasalin Nijeriya, na cikin dokokin da majalisun dokokin ƙ asar nan ke aiki akan su, kuma a kwanakin baya, an riga an kaɗa kuru’a a majalisun, inda ra’ayi ya fito a fili cewa ba a goyan bayan da yawa daga cikin bukatun ‘yan a  sauya fasali. Misali dokar rage ma gwamnatin Tsakiya ƙ arfi,wato De ɓ olution of power a turance, dukan majalisun dokokin Nijeriya sun yi watsi da kuɗirin, abin da bai ma ‘yan bokon kudu dadi ba. Domin hatta ga yadda aka kaɗa kuri’a, ya fito fili da bambance-bambance dake tsakanin wakilan Arewa da na kudu. Wakilan Arewa Arba’in da takwas (48) a majalisar dattawa sun yi watsi da batun rage ma gwamnatin tsakiya ƙ arfi,inda wakilan kudu Arba’in da bakwai (47) suka amince da kuɗirin, wannan ya nuna da kuru’a daya tak, Arewa tasha daga faɗawa cikin jangwangwama.

Kazalika batun cire tsarin aikin yima ƙ asa hidima daga kundin tsarin mulki,da batun dokokin da suka shafi mallakar ƙ asa ko fili, da batun iyakokin ƙ asar,duk basu samu tagomashi a garambawul din da a ke ƙ oƙ arin yi ma kundin tsarin mulki ba.

A ganinmu, wannan nasara ce babba ga Nijeriya, musamman Al’ummar Arewa, tunda da ‘yan a sauya fasali sun samu nasara, an rage ma gwamnatin tsakiyar ƙ arfi, to da za mu koma baya,tsarin da zai baiwa yankuna ƙ arfi fiye da gwamnatin tsakiya. Mu fahimta, irin wannan tsari da zai ba yankuna ƙ arfi fiye da gwamnatin tsakiya, an taba yin sa a ƙ asar Amurka daga 1781 zuwa 1789, a lokacin Amerika ta faɗa cikin ruɗani, ya zamana gwamnatin Tsakiya sai ta yi bara wurin manyan yankuna sannan za ta iya biyan albashi. Kazalika, ‘yan ƙ asar Amerika suka faɗa ruɗani akan wace gwamnati za sui ma biyayya? Ta yankunansu koko ta tsakiya? Domin irin wannan tsari yakan ba yankuna kwarya-kwaryar cin gashin kai,wani lokaci ma, kowa ce shiyya ko jiha za ta samar da kundin tsarin mulkinta,’yansandanta,ta kuma mallake duk arzikin dake yankinta, ciki harda duk wani nau’i na haraji. Za a fito ne kawai da tsari da zai ce kowace shiyya ko jiha za ta ba gwamnatin tarayya wani kaso daga cikin abin da take samu.Wannan yana haifar da makeken gibi tsakanin jihohi masu arziki da matsiyata, inda wani bangare na ƙ asar zai kasance cikin kunci da koma baya,wani bangaren zai zama mai dimbin arziki da ci gaba. Wannan matsalar a ƙ arƙ ashin irin wannan salon mulkin, tana faruwa hatta a manyan ƙ asashe masu ci gaban masana’antu. To saboda dimbin matsaloli na wannan tsari da a turanci ake ma laƙ abi da confederacy, ya sanya dole Amurka ta watsar da shi, ta rungumi tsarin tarayya wanda ya dace da bukatun Amurka.Kuma hakan ya taimaki  Amurka musamman a lokacin yakin basasarta da tai daga 1861 zuwa 1865. To wancan tsarin ne fa, wasu yanzu ke so mu koma? Kazalika, muma a Nijeriya, a jamhuriya ta farko kusan tsarin da muka bi kenan, to amma su ‘yan boko da ‘yan siyasar kudu waɗanda su kai ta ƙ ulla makirci wa gwamnatin su Tafawa Balewa har Sojoji suka shigo su kai juyin mulki suka kashe shugabannin Arewa, sune suka rusa wancan shiri. Kuma Aguyi Ironsi wanda shi ne ya zama shugaban mulkin soja na wancan lokaci shi ne ya rusa wancan tsari inda ya kafa wata doka mai lamba 34. Wato Decree No. 34 wanda ya kawo karshen wancan tsarin da yankuna ko shiyyoyi ke da ƙ arfi. To kuwa dole mu jefa ayar tambaya, me yasa a wancan lokaci, mutanen kudu su kai kutinguilar da ta kawo karshen wancan tsari,da yanzu kuma suka dage dole sai mun koma mai?

Wannan ya kawo mu ga dalilan da yasa, ‘yan siyasa da sauran jami’an kudu ke ta kiraye-kirayen a zo a sauya fasali.

Na farko duk wanda ya kalli ƙ asar nan da kyau, zai ga Kudu maso Yamma da ta ƙ unshi jihohin Lagos, Oyo, Ogun, Ondo,Osun da Ekiti ita ce ke da mafi yawan arzikin dake Nijeriya. Duk wasu manyan kamfanoni da suka ƙ unshi na sarrafa ƙ arafa, siminti, filawa, sukari, cakulat, katifu, robobi, sinadaran haɗe-haɗe, kamfanonin magunguna, taba sigari, kamfanonin sadarwa, su ke da cibiyoyin kasuwanci na ƙ asa da ƙ asa, waɗanda ke samar masu da ɗimbin haraji. Manyan lauyoyi, injiniyoyi, masu zana taswirar gini, kamfanoni masu bada shawarwari (consulting firms), manyan gidajen jaridu duk sune cunkushe a wannan yanki na kudu maso Yamma. Kazalika ga su da manyan tasoshin jiragen ruwa da suka haɗa da Apapa da Tin Can. Duk idan aka koma tsarin da suke so, to duk wani haraji ko kuɗin shiga daga waɗannan kamfanoni zai dinga faɗawa lalital shiyyar ne, inda za su dinga kwantala ma gwamnatin tsakiya dan abinda suka ga dama domin ta kula da batun tsaro, difilomasiyya da shige da fice. Kuma za su mamaye duk wasu  gurabun ayyuka da za a samu a waɗannan cibiyoyi, sannan tunda suna da damar yin dokoki, za su tsawwala ma baƙ i, musamman mutanen Arewa waɗanda ke zaune can, duk sai sun hurgado su,domin ma a yanzu ya aka kare balantana an sauya fasalin ƙ asar.

Jihohin Kudu maso Gabas da suka ƙunshi Jihohin Imo, Abia, Anambra, Enugu da Ebonyi, sune ke da babbar kasuwar Aba, kuma Inyamurai sune suke rike da harkar kasuwancin Nijeriya. Sun mamaye kowane bangare ciki harda harkar sayar da magunguna, fenti, siminti, litattafai da kayan karatu, kayayyakin wutar lantarki, harkar sufuri, takalmi, sutura da komi ma. Ta baƙ in shugaban ƙ ungiyar Inyamurai na duniya, ya ce sun zuba jarin kusan Tiriliyon hudu a sassa daban-daban na Nijeriya. Kuma jihohi irin Abiya da Imo suna da arzikin man fetur.

Amma idan muka kalli Arewa, za mu ga, masana’antunmu sun mutu, noman da muke takama da shi har yanzu irin na kaka da kakanni ne, wanda ba irin shi a ke a inda noma ke kawo kuɗi masu kabri-kabri ba. Sannan a harkar noman da kiwo, an zo an  kitsa rikici tsakanin manoma da Fulani, inda kiwon da noman na neman gagararmu. Ga batun sauyin yanayi. Ga nau’inka tashe-tashen hankula daban-daban kamar rikicin boko haram, masu garkuwa da mutane da sauran su. Sai kuma a zo yanzu gatse-gatse a ce so a ke ai mana shirme?

 

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Minti Biyar Da Matar Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Hadiza Masari

Next Post

Rashin Ilimi Ne Ya Sa Aka Bar Mata A Baya -Amina Gwamna

RelatedPosts

Sarkar Da Za Ta Sarke Kaduna Bayan Amsar Bashin Dala Miliyan 350 Daga Bankin Duniya

Sarkar Da Za Ta Sarke Kaduna Bayan Amsar Bashin Dala Miliyan 350 Daga Bankin Duniya

by Sulaiman Ibrahim
55 mins ago
0

Daga Dr. Nasiru Aminu “Babu al’ummar da za ta kasance...

National Economy

Shekara Daya Da Fara Fitowa: Gudumawar Jaridar NATIONAL ECONOMY Ga Tattalun Azikin Nijeriya

by Muhammad
5 days ago
0

Daga Khalid Idris Doya, A jiya Asabar ne jaridar NATIONAL...

Mata

Kayan Da’a Na Mata: Illa Ko Amfani? (3)

by Muhammad
5 days ago
0

Daga Sameerah Bello Shinko, 08025729364: Hana daukar Ciki: Wasu maganin...

Next Post

Rashin Ilimi Ne Ya Sa Aka Bar Mata A Baya -Amina Gwamna

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version