Musulmai Da Yahudawa Na Bikin Shekara 200 Da Kulla Kawance A Bosnia

Musulmai da Yahudawa a kasar Bosniya na bikin cika shekara 200 da kulla kawance.

Suna shagulgulan cika shekara 200 ne a wani biki da aka yi wa lakabin Sarajebo Purim, lokacin da al’ummar Musulmi suka kubutar da rukunin wasu shugabannin Yahudawa daga gidan yarin Daular Ottoman.

Shugabannin al’umma a yanzu na cewa wannan wani misali ne da ya kamata duniya ta yi koyi.

Tun shekaru da dama da suka gabata Sarajebo ya shahara a daya daga cikin yankunan Turai da ke da mutane mafi hakurin zama da juna.

Musulmai da Yahudawa da Kiristoci daga dariku daban-daban ne suke huldodinsu cikin kwanciyar hankali da juna a babban birnin kasar na Bosniya.

Shekara 200 da ta wuce sun taba tashi tsaye suka kare makwabtansu lokacin da gwamnan Sarajebo na Daular Ottoman ya yi garkuwa da shugabannin al’ummar Yahudawa, inda dubban Musulmai suka taru suka kubutar da su.

Ba a taba mantawa da wannan lamari ba, duk da yake-yaken duniya biyu da aka tafka da kuma masifar rikicin da kasar ta fuskanta cikin shekarun 1990.

Bikin cika shekara 200 din yana jaddada kawancensu ne.

Shugaban al’ummar Yahudawan Bosniya Jakob Finci ya yi tambayar cewa, “Shin idan za su iya zama lafiya da Musulmai, me ya sa kowa ma ba zai iya yin haka ba a duniya?”

Shi ma takwaransa jagoran Musulmai Husein Kabazobic, ya ce “Karuwar kyamar da ake nunawa al’ummar Musulmai ta sa ya zama muhimmin abu su sabunta alkawarinsu na cewa za su kasance abokan makwabtaka nagari.”

Exit mobile version