Al’ummar Musulmai da ke yankin Yolan Bayara a Jihar Bauchi, ta rubuta takardar korafi kan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na bai wa Kiristoci wani katafaren filin makabarta da Musulman suka ce mallakinsu ne.
Musulman sun rubuta wasikar koken ne a ranar 10 ga wannan wata na Janairu zuwa gwamnan Jihar, Sanata Bala Mohammed ta wasikar sakataren gwamnatin jihar.
- Atiku Ba Ya Tsoron A Bincike Shi – Dino Melaye
- Dabarun Kasar Sin Na Yaki Da COVID-19 Sun Bunkasa Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya
A cikin wasikar, an kuma yi kwafin hukumomin tsaron jihar da Sarkin Bauchi da shugaban Kungiyar Jama’atu Nasril Islam, reshen Jihar Bauchi da shugaban Kungiyar Izala ta JIBWIS, reshen Jihar Bauchi, yayin da Musulman suka bukaci daukar matakin gaggawa domin hana barkewar rikici tsakanin al’ummar jihar.
A yayin mayar da martanin gaggawa, mai magana da yawun gwamnan Jihar Bauchi, Mukhtar Gidado, ya bayyana cewa, kawo yanzu gwamnati ba ta mika filin ba mai fadin kadada 470 ga Kiristocin, yana mai cewa, har yanzu, gwamnati na ci gaba da nazari kan lamarin.
A makon jiya ne, al’ummar Kirista karkashin jagorancin shugaban kungiyar CAN a Bauchi, Rabaran Dakta Abraham Demius Damina, ya bayyana cewa, gwamnan jihar ya ba su kyautar fili mai fadin kadada 50 domin amfani da shi a matsayin makabarta.