Sayyid Isma’il Umar (Mai Diwani) 08051529900 (Tes kawai)
Muna farawa da gaisuwar Musulunci ga daukacin al’ummar Musulmi, da Muminai da kuma Muhsinai, ita ce Assalamu Alaikum wa Rahmtullahi Ta’ala wa Barkatuhu. Musulunci addini ne mai matakai guda uku ko kuma a ce Hadarorin Allah guda uku kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya bayyana a cikin Hadisin da Sayyidina Mala’ika Jibrilu (AS) ya zo masa a siffar Dan Adam ya tambaye shi.
A ruwayar da ta zo daga Sayyidina Umar (RA), ya ce “wata rana muna zaune a gaban Manzon Allah (SAW) sai wani mutum ya bullo a gare mu, mai tsananin farin tufafi, mai tsananin bakin gashi, babu wata alamar tafiya daga gare shi kuma babu mutum daya a cikinmu da ya san shi, har ya zo ya zauna a wajen Manzon Allah (SAW) ya hada gwiwarsa da na Annabi, ya dau tafukan hannunsa ya dora a kan cinyar Annabi (SAW) ko kuma a kan cinyarsa. Ya ce “ya Muhammad, ba ni labarin mene ne Musulunci”.
Kafin mu kawo amsar da Manzon Allah (SAW) ya bashi, bari mu dubi irin yanayin da wannan bako ya zo wurin Annabi (SAW) da shi.
Sayyidina Umar yana bayyana mana irin yadda wannan mutumin ya zo da abubuwa na al’ajabi. Wurin da ya ce ya bullo mana, yana nufin ba wai ya zo yana tafe ne kamar yadda mutane ke zuwa ba, kawai kamar kana zaune kim; sai ka ga wani abu kurum a gabanka. Da ya ce “mai tsananin farin tufafi”, ma’ana a irin wannan zamani da babu kayan ado sosai, mutum zai yi shekaru yana amfani da riga guda daya, koda fara ce sai ka ga ta dafe, amma shi mutumin kayan shi farare ne sal-sal kamar a lokacin aka kera su. Ma’anar mai tsananin bakin gashi kuma, yana nufin gashin kansa baki ne sidif duk da a wannan lokacin gashin kan Larabawa idan an yi tafiya mai nisa za a ga ya yi kura sosai ya zama birkata-gashi, amma shi nashi kamar yanzu ya fito daga wurin gyaran gashi (saloon).
Irin kiran da Mala’ika Jibrilu ya yi wa Annabi (SAW) da ya ce “ya Muhammad” kira ne na ‘wauta’ domin janyo hankalin Sahabbai kan abin da zai gudana a tsakaninsa da Annabi (SAW), ba kuma hakan yana nufin Mala’ika Jibrilu wauta ya yi ba, a’a; muradinsa shi ne duk wanda yake zaune a wurin hankalinsa ya dawo wurinsu. Su Sahabbai ba sa masa irin wannan kiran, Allah ya ce “kar ku rika kiran Manzo kamar yadda sashenku ke kiran sashe…”. Allah (SWT) ma da ya halicce shi (SAW) sai dai ya ce masa “ya ayyuhar Rasuulu, ya ayyuhan Nabiyyu da sauransu”. Amma shi Mala’ika Jibrilu ya yi masa wannan kiran ne don hankalinsu ya dawo jikinsu har su yi tunanin wai waye ya zo ne kuma ya yi wa Annabi irin wannan kiran.
Za mu cigaba da bayanin Hadisin. Da Mala’ika Jibirilu (AS) ya tambayi Manzon Allah (SAW) mene ne Musulunci? Sai ya ce, “Musulunci shi ne ka shaida babu wani Ubangiji sai Allah, ka tsaida Sallah, ka ba da Zakka, ka yi Azumin Ramadan, ka yi Hajji idan Allah ya sa ka samu iko”.
Ma’anar wannan shi ne, duk wanda yake aikata wadannan abubuwan da aka lissafo shi ne ake kira da “Musulmi”. Kuma duk abin da Allah ya alkawarta wa Musulmi insha Allahu zai samu. Wannan Hadisin na Jibrilu kusan a duk makarantun Islamiyya ana karantar da shi. Da za a dawo aiki da Hadisin duk wata rigima a tsakanin Musulmi za ta kau. Domin an fadi yadda Musuluncin yake kuma duk wanda ya yi riko da abin da aka fada a kan Musuluncin shi ne Musulmi sannan babu wani mahaluki da yake da ikon ya kore shi a Musuluncin. Duk zunubin da yake aikatawa matukar ba ya ce Allah yana da abokin tarayya ba Musulmi ne, sai dai a ce masa mai aikata ‘kaba’ira’ wato babban laifi. Kuma idan ya mutu ba za ka ce ma sa danwuta ba; sai dai ka ce ya tafi Mashi’ar Allah, idan Allah ya ga dama ya gafarta ma sa; idan ya so ya azabtar da shi. Kai kuma da za ka nuna Imanin Musulunci sai ka roka ma sa gafara ba neman azabtar da shi ba. Wannan shi ne Musulunci.
A wannan Hadisin an ce “shaidawa babu wani Ubangiji sai Allah”, amma akwai wani Hadisin da Manzon Allah (SAW) ya ce “an umurce ni in yaki mutane har sai sun fadi La’ilaha illallah”. Ka ga a nan fada da baki kawai aka ce, babu binciken abin ya shiga zuciya ko bai shiga ba. Toh, da iya abin da Manzon Allah (SAW) ya lissafa a ma’anar mene ne Musulunci kenan, wato Shaidarwar La’ila ha illallah, da Sallah, da Zakka, da Azumi da kuma Hajji su kadai ne Musulunci kawai, mai tambayar nan sai ya tashi ya tafi tunda an bashi amsa kuma har shi ya gaskata Manzon Allah (SAW) a kan haka. Sayyidina Umar (RA) ya ce “muka ji mamakin sa saboda yana tambaya kuma yana gaskatawa”, ma’ana ashe dama yana da masaniyar abin da yake tambaya kenan.
Da yake ba a nan matakin Musulunci ya tsaya ba kawai, sai ya kara tambayar Manzon Allah (SAW) a kan mataki na gaba. Ya ce “to mene ne Imani?”.
Bisa wannan tambayar, ashe Musulmi ‘kawai’ ba shi ne mai imani ba? A’a, Allah ya ce ba haka ba ne. Wasu Larabawan kauye sun zo wurin Annabi (SAW) suna so su yi ma sa kwarkwara suna cewa “mun yi imani”, amma Allah ya ce a’a, “ba ku yi imani ba, ku dai ku ce mun musulunta, (shi imani tukuna) har sai ya shiga cikin zuciyarku”. Dama da zaran an fara zancen abin da ke cikin zuciya to yanzu maganar imani ta shigo.
Don haka da Mala’ika Jibrilu ya tambayi Manzon Allah (SAW) mene ne Imani? Sai ya ce Imani shi ne “ka yi imani da Allah (duk abin da Allah ya fada ka yi imani da shi, kamar misali; Allah ya ce yana tare da mu a duk inda muke, toh, walau mun gane ko ba mu gane ba mu dai mu yi imani da hakan, kar a damu da masu cewa duk wanda ya ce Allah yana ko ina ya mayar da Allah ‘billions’, subhanallah. Masu fadar wannan ba su fahimci Kudurar Allah ba, da sun gane, ko fasahar wannan zamanin (technology) sai ta kunyata su musamman idan za su yi la’akari da Gidan Talabijin. Mutum daya ne za ka ga yana karanta labaru amma talabijin bila’adadin ke nuna shi kuma wannan bai sa ma’aikacin ya zama da yawa ba. Bature wanda yake Halittar Allah shi ne ya yi wannan fa, to ina ga Rabbul Izzati (SWT)? Mu yi imani kawai)
“Da imani da Mala’iku (halittun Allah masu fukafuki da aka halicce su da haske. Mala’ika Jibrilu shi kadai yana da fukafuki dubu dari shida, kowane fuffuke zai rufe duniya. Amma ya ce idan ya zo gaban Mala’ika Mika’ilu (AS) kamar kwai ne a gaban giwa. Masu kissa suna fada mana cewa, wata rana Mala’ika Jibrilu (AS) ya nemi Allah (SWT) ya yi ma sa izini ya bude fukafukansa dubu dari shidan nan ya yi gudu ya tashi yadda yake so. Allah ya yarda ma sa. Sayyidina Jibrilu (AS) ya bude fukafukan nan nasa ya tashi ya yi gudu har ya gaji, sai Allah ya ce ma sa “ka san a ina kake (tun daga wurin da ya tashi har zuwa wurin da ya sauka”, ya ce “a’a”, Allah ya ce “a tsakanin dumbarun bakin wani Mala’ika ne zuwa zozar hancinsa”, ma’ana duk a iya nan ya yi wannan gudun. Babu wanda ya san yawan rundunar Allah sai dai shi (SWT). Akwai Mala’ikan da kafarsa ma tana can karkashin kasa ta bakwai ne amma kansa yana bayan Al’arshi. Ka ga ai ya shige ta duniyar nan tamu amma ba mu ga wani tudu da ya rufe wani wuri ba a matsayin jikin wannan Mala’ikan, amma kuma mun yi imani akwai shi. Duk da irin wannan girman na Mala’iku kuma sai mu ji Manzon Allah (SAW) ya ce guda dubu saba’in sun shigo soronsa. Ka ga a nan dole sai da imani. Kodayake fasahar wannan zamanin ta yi mana isharar abubuwa da yawa. Misali, kowannenmu (ban da jarirai) girmansa ya fi na Talabijin amma kuma idan aka dauke mu da ‘camera’ sai a nuno mu a cikin Talabijin din ba tare da an rage tsawonmu ko kibar jikinmu ba.
“Wani ya taba tambayar Sayyidina Aliyu (Allah ya girmama fuskarsa) cewa “ya Imam, shin Allah yana da iko ya shigar da duniyar nan bakidaya cikin kwai ba tare da ya rage duniyar ya motse ta ba kuma ba tare da ya kara wa kwan girma ba?”
Za mu cigaba a mako mai zuwa albarkar Annabi (SAW). Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadiy wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil azim