Wasu mutane 11 sun kone kurmus a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da ababen hawa daban-daban a yankin Ochadamu a Jihar Kogi.
Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta sanar sa hakan cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, cewa hatsarin ya rutsa da ababen hawa 20.
- El-rufai Ya Amince Da Nadin Wazirin Garin Jere A Matsayin Sabon Sarkin Masarautar Jere
- Hadin Gwiwar Sin Da Afrika Kan Tattalin Arzikin Zamani Ya Baiwa Afrika Damammaki Masu Kyau
Kakakin FRSC, Bisi Kazeem, ya ce za a iya kare afkuwar haduran, yana mai kira ga masu ababen hawa da su dinga kula da abin hawan nasu akai-akai.
“Tawagar bincike ta ba da rahoton cewa lamarin ya rutsa da mutum 18.
“Daga cikinsu, mutum bakwai – uku maza hudu mata – sun ji raunuka daban-daban – yayin da sauran 11 din wadanda ba a iya tantance jinsinsu ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton sun kone kurmus.”
Ya kara da cewa rahoton ya bayyana dalilin faruwar hatsarin da lalacewar titi, da shanyewar birki, da rashin ingancin abin hawa.