Akalla mutane 12 ne suka mutu a wani turmutsutsun jama’a a wani filin wasa da ke Antananarivo babban birnin kasar Madagascar, in ji Firayim Minista Christian Ntsay.
Kazalika mutane 80 sun jikkata a yayin bikin bude gasar wasannin a filin wasa na Mahamasina.
- Shugabannin Sin Da Madagascar Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafuwar Dangantakar Dake Tsakanin Kasashen Su
- Firimiyar Bana:Wasanni Uku Da Za Su Fi Daukar Hankalin Masu Kallo
Jami’in kungiyar agaji ta Red Cross Antsa Mirado ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “Mutane da yawa sun cunkushe a kofar shiga filin wasannin.”
Shugaba Andry Rajoelina, wanda ke filin wasan, ya ce wannan lamari ne mai ban tausayi, ya bukaci yin shiru na minti daya don nuna jimaminsu kan wadanda ibtila’in ya rutsa da su.
Filin wasan Mahamasina – mai ɗaukar mutane kusan 41,000 – an ba da rahoton ya cika makil da ‘yan kallo.
Hotunan da suka fito sun nuna wasu da dama da suka jikkata a zaune a kasa.