Rundunar ‘yansandan jihar Kano, ta kai samame kasuwar canjin kudi ta Wapa, inda ta kama mutane 17 da ake zargi da yin hada-hadar canjin kudi ba bisa ka’ida ba.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.
- CBN Ya Bukaci Masu POS Su Yi Rajista Da Gwamnati
- Sojojin Nijar Sun Kama Kasurgumin Dan Bindigar Da Ya Addabi Nijeriya, Kachallah Mai Daji
Kiyawa ya ce rundunar ta kai samamen ne tare da hadin gwiwar jami’an hukumar DSS.
A cewarsa, tun da farko mutane 29 rundunar ta kama, amma ta saki mutane 12 daga cikinsu bayan gaza samun cikakkiyar hujja a kansu.
Ragowar mutane 17 da aka kama an gano kudin CFA kimanin dubu 68 sai kudin Indiya, Rupees 30.
Bincike ya nuna mutanen 17 da ake zargi suna aiki ne karkashin wani kamfanin da ba shi da rajista da gwamnat.
Kiyawa, ya ce sun kai samamen ne don yaki da masu hada-hadar canjin kudi ba bisa ka’ida ba, da nufin kawo tsafta cikin harkar.
Kazalika, ya ce rundunar za ta gurfanar da su a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.