Gwamna Dauda Lawal, a jiya Laraba, ya kaddamar da shirin farfado da tattalin arziki na shirin (N-CARES) na Nijeriya Coronavirus (COVID-19) tare da rarraba kayan amfanin gona da kadarorin noma ga mutane 19,000.
An gudanar da bikin kaddamar da shirin na Fadama III a ma’aikatar noma ta Jihar Zamfara, kuma mutane daga kananan hukumomi shida ne suka amfana da shirin.
- Masu Fyade Da ’Yan Luwadi 369 Aka Kama A 2023 A Katsina
- Tsohuwar Ministar Ayyukan Jin-Kai Ta Ki Amsa Gayyatar EFCC
A wajen bikin an raba sama da injinan wutar lantarki 700 da iri na shinkafa da masara ga manoma 19,000.
A cewarsa, gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta kuduri aniyar inganta harkar noma ta hanyar samar da isasshen tallafi ga manoma.
A yayin jawabinsa a wajen taron kaddamarwar, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da ayyukan yi ga marasa karfi a Zamfara.
Ya ce: “Ta hanyar shirin Fadama III, manoma 100,000 ne za a karfafa musu kayan aiki da iri a cikin shekaru hudu masu zuwa, kuma wannan yana ciki kasafin kudin cetonmu na 2024, ya shaida kudurisa na daukar matakan da ake bukata domin ganinmun cimma burinmu a fannin noma, wanda shi ne bangare mafi muhimmanci na tattalin arzikin jiharmu.
“Kamar yadda kuka sani, shirin COVID-19 shiri ne na farfado da tattalin arziki shiri ne da ya kunshi bangarori daban-daban da ke kewaye da yankuna uku masu muhimmanci kuma an tsara shi don magance kalubale da samun damar yin amfani da damar inganta noma.
“A karkashin FADAMA 3, yankin zai mayar da hankali ne kan inganta samar da abinci da kuma tabbatar da amintaccen aikin samar da abinci ga gidajenmu masu rauni.”
Bugu da kari, Gwamna Lawal ya ce gwamnatin Jihar Zamfara za ta bayar da tallafi da ayyuka masu muhimmanci, da ginawa da gyara hanyoyin shiga, tare da ware kadarori domin noma da rage asarar abinci”.
“A wannan zagaye na uku, babban burinmu shi ne mu inganta ayyukan noma 11,760 kai tsaye ta hanyar samar musu da muhimman abubuwa kamar takin zamani, maganin ciyawa, maganin kwari, ingantattun iri, da sinadarai masu sanya iri. Domin noman rani mai zuwa, mun ware buhunan taki 33,000 – wanda ya kunshi buhunan NPK 22,000 da kuma buhunan Urea 11,000.
“Haka zalika, za a raba injinan wutar lantarki sama da 700 da iri na shinkafa da masara ga manoma 19,000. Bugu da kari, kungiyoyi 735 na manoma goma kowannen su za a ba su na’urar wutar lantarki, kuma mutane 2,550 za su karbi kananan dabbobi.”