Kusan mutane 6,000 ne suka ci gajiyar Zakka ta Naira miliyan 132 da masarautar Hadejia ta jihar Jigawa ta raba a shekarar 2023.
Kakakin Majalisar, Alhaji Muhammad Talaki ne ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Dutse, ranar Laraba.
- Ya Kamata Kasashen Yamma Su Yi Tunani Kan Laifinsu
- ‘Yan Sa-kai Za Su Taka Rawa Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro A Arewacin Nijeriya – Yusha’u Kebbe
Ya ce, kayayyakin da aka raba na zakkar sun hada da tsabar kudi da hatsi da kuma dabbobi.
Talaki ya ce, Shugaban kwamitin tattara Zakka na yankin, Alhaji Abdulfatah Abdulwahab ne ya sanar da hakan a lokacin da ya kai ziyara a wajen kaddamar da rabon zakka na shekarar 2024 a yankin, a ranar Talata.
“Kwamitin Zakka na Masarautar Hadejia ya tara tare da raba Zakka da ta kai naira miliyan 132 a yankin a shekarar 2023.”
Abdulwahab ya bayyana haka ne a lokacin da yake duba yadda aka gudanar da atisayen a lokacin kaddamar da rabon zakka na bana a fadar sarkin Hadejia.