Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Kogi, ta tabbatar da mutuwar mutane takwas a wani hatsarin da ya afku a garin Ankpa na jihar.
Kwamandan hukumar a Jihar Kogi, Stephen Dawulung, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wata motar dakon mai da motoci uku da babura uku ne suka yi hatsarin.
- NECO Ta Saki Sakamakon Jarabawar 2022
- Shirin Twitter Space Na LEADERSHIP Hausa: Yadda ‘Yan Nijeriya Za Su Kauce Wa Komawa ‘Yar Gidan Jiya A Zaben 2023
A cewarsa, hatsarin ya afku ne lokacin da wata tankar mai dauke da mai ta rasa birki tare da murkushe wasu motoci uku ciki har da babura uku kafin ta fadi a kan gada sannan ta kama wuta.
Kwamandan ya kara da cewa, hatsarin ya afku ne da misalin karfe 11;30 na safe, kuma mutane takwas suka mutu yayin da aka ceto wasu mutane biyu da ransu kuma an kai su asibiti a garin Ankpa domin yi musu magani.
Ya kuma bayyana cewa an zakulo gawarwakin mutane takwas din daga wurin da hatsarin ya afku.
Kwamandan, ya bukaci direbobin tankar mai da su sanya abin da zai ke hana motocinsu zubewar mai a kasa.
Ya kuma bukaci direbobin da suke daukar hakikanin man da motar za ta iya dauka, tare da daina bai wa yaransu tukin motoci a manyan tituna.