Tankar mai ta yi bindiga a ranar Asabar a yankin Ugwu Onyeama, a ƙaramar hukumar Udi a Jihar Enugu, inda ta hallaka mutane da dama.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safe, lokacin da tankar man fetur ta kama wuta a kan hanya.
- Salmai Albasu: Mawakiyar Da Ta Rera Wakar Soriye Ta Cika Shekara 70
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Gudanar Da Liyafar Sabuwar Shekara
Gobarar ta ƙone motocin da ke gefen hanya, kuma an ce mutane da dama sun ƙone ƙurmus.
Hukuma ba ta tabbatar da adadin waɗanda suka rasa rayukansu.