Ya zuwa yau Laraba, adadin mutanen da suka rasu sanadiyyar girgizar kasa mai karfin maki 6.8 da ta auku a gundumar Luding ta lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin ya karu zuwa 74, wasu 26 sun bace, kana mutane 259 suka ji rauni.
Yanzu ana nazarin yanayin da yankin ke ciki, da kuma gudanar da aikin ceton gaggawa. Kasar Sin kuma ta yi amfani da rukunin taurarin dan adam na Gaofen, don taimakawa aikin agaji, sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 6.8 da ta afku a lardin Sichuan dake yankin kudu maso yammacin kasar.
A cewar tsarin sa ido kan yanayin duniya, da cibiyar tattara bayanai ta hukumar kula da harkokin sararin samaniya ta kasar Sin (CNSA), sama da taurarin dan adam 10 ne aka tura, domin daukar hotunan wuraren da girgizar kasar ta afku, mintuna 10 bayan girgizar kasar da ta afku a gundumar Luding dake lardin Sichuan da karfe 1 saura minti 8 na yammacin ranar Litinin, ciki har da rukunin taurarin dan adam na Gaofen-3 mai lamba 01, da mai lamba 02, da mai lamba 03, da tauraron dan adam na Gaofen-1 D, da tauraron dan adam na Gaojing-1, matakin da ya taimaka wa kwararru wajen yin nazarin bayanai, da kara fahimtar yanayin lalacewar wadannan yankuna.
Hukumar CNSA za ta ci gaba da aika taurarin dan adam na farar hula da na kasuwanci, don tallafawa rigakafin aukuwar bala’i da ayyukan agaji, da bayar da tallafin bayanai game da sararin samaniya, don sa ido kan aukuwar bala’i da daukar matakan da suka dace. (Jamila Ibrahim Yaya)