Nasir S Gwangwazo" />

Mutanen Neja Sun Yi Murna Da Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Matan Karkara 

Mutanen Neja

Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya bayyana farin cikin sa kan yadda aka raba kudi naira miliyan tamanin ga matan jihar su 4,000 a karkashin shirin tallafa wa matan karkara da jari wanda Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa.

Gwamnan ya fadi haka ne lokacin da Ministar Harkokin Jinkai Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ta kai ziyara jihar a ranar Asabar.

Gwamnan ya ce shirin na ‘Cash Grant for Rural Women’ zai taimaka wa matan jihar da dama wajen ficewa daga kangin fatara da yunwa.

Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Ahmed Ibrahim Matabele Alli, ya wakilta, ya ce tallafin ya zo ne a daidai lokacin da jama’ar Jihar Neja su ke fama da fatara sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga ke kai masu ba kakkautawa wanda hakan ya sanya da yawan su sun koma sansanin ‘yan gudun hijira da zama, da satar shanu da kuma annobar korona da ta zo a watannin baya.

Ya ce ya tabbatar matan za su yi amfani da tallafin wajen inganta rayuwar su.

Ya ce, “Na gode wa mai girma Shugaban Kasa da ya kawo wannan tsari na taimakon matan karkara a duk fadin kasar nan ta hanyar wannan Tallafi na Musamman.

“Mu na godiya kan dukkan tsare-tsare na Gwamnatin Tarayya da aka ba wannan jiha saboda ambaliya, hare-haren ‘yan bindiga, shirin ‘Conditional Cash Transfer’, ‘GEEP’, ‘N-Power’ da kuma ‘Home Grown School Feeding Programme’ da sauran su.

“Har yanzu mu na bukatar karin taimako a Jihar Neja. Mutanen mu sun kara shiga cikin matsin fatara saboda yanayin rashin tsaro da ‘yan bindiga su ka janyo, da satar shanu da sauran matsalolin rayuwa.

“Duk da haka, ina tabbatar maku da cewa wadannan matan za su yi matukar amfani da wannan tallafin kudin da aka ba su.”

Tun da farko a wajen kaddamar da shirin a jihar, sai da Minista Sadiya Umar Farouk ta bayyana cewa shirin bada kudin tallafin wani bangare ne na shirye-shiryen gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na ceto fakirai daga tarkon fatara.

Ta ce, “Ran ka ya dade, a matsayin wani sashe na yunkurin Gwamnatin Tarayya na kawar da fatara da yunwa a fadin kasar nan, an fito da babban Shirin Agajin Jama’a na Kasa, wato ‘National Social Inbestment Programmes’ (NSIP) da zai inganta rayuwar wadanda su ka fi kowa talauci a kasar nan kuma ya na daga cikin manyan tsare-tsaren yaki da talauci a Afrika.

“A matsayin wani bangare na tsinkayar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin fatara cikin shekaru 10, Gwamnatin Tarayya ta hanyar ma’aikata ta ta shigo da Shirin Bada Tallafin Kudi ga Matan Karkara wanda mu ke kaddamarwa a yau. An tsara shi ne ta yadda za a yi biyan kudi N20,000 sau daya ga matan da su ka fi kowa kasancewa cikin fatara a yankunan karkara a Nijeriya don sama masu hanyar karbar kudin da za su ja jari domin su fara sana’a.

“Ana raba kudin ne ga matan karkara su sama da 150,000 a duk fadin jihohi 36 na kasar nan da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya.”

Da ma can ita Jihar Neja an riga an ba ta jimillar kudi N1,991,070,000.00 (naira biliyan daya da miliyan dari tara da casa’in da daya da dubu saba’in) daga shirin Gwamnatin Tarayya na Tallafin Tiransifar Tsabar Kudi, wato ‘Conditional Cash Transfer’ (CCT), wanda ya shafi rayuwar gidajen mabukata guda 43,611 (PBHHs).

Kananan hukumomi 12 da su ka hada da Wushishi, Chanchaga, Bida, Kontagora, Rafi, Bargu, Agaie, Mashegu Katcha, Bosso, Munya, Lapai, da Labun a yanzu duk su na amfana da wannan shirin Gwamnatin Tarayya na CCT a Jihar Neja.

An zabo masu cin moriyar shirin bada tallafin kudi ga matan karkara ne daga kananan hukumomi 25 na jihar.

Manyan baki a wajen taron kaddamarwar sun hada da karamin Ministan Harkokin Kasashen Waje Ambasada Zubair Dada, da Darakta Janar na hukumar NEMA, ABM Muhammadu Alhaji Muhammed, da Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Neja, Alhaji Muhammed Abdullahi Bawa Wuse wanda shugabar Kwamitin Mata na majalisar, Hajiya Binta Mamman ta wakilta, da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Neja, Hajiya Salamatu T. Abubakar, da Daraktan Kudi da Gudanarwa mai kula da NSIP a Ma’aikatar Harkokin Jinkai, Malam Abdullahi Musa Yusuf, da jami’ar kula da shirin tallafi a Jihar Neja kuma mai bada shawara na musamman kan shirye-shiryen agaji, Barista Amina Musa Gu’ar, da Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Neja, Hajiya Tasalla Fati Ibrahim, da sauran jagororin mata.

Exit mobile version