Ma’aikatan jirgin ruwa biyu ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu tara suka bace a ranar Laraba bayan da jirgin dako ya nutse a cikin ruwa tsakanin kasar Japan da Koriya ta Kudu, in ji hukumomin Japan.
Jami’an tsaron gabar teku na kasashen biyu, tare da jirgin soji da wani jirgin ruwa mai zaman kansa, sun gano 13 daga cikin mutane 22 da ke cikin jirgin Jin Tian, kamar yadda wani jami’in tsaron gabar ruwan Japan ya bayyana.
- An Fara Aiki Da Sashen Farko Na Layin Dogon Da Sin Ta Gina A Lagos
- Da Dumi-Dumi: Dan Takarar Gwamnan Jihar Abia Na Jam’iyyar PDP Ya Rasu
Amma daga baya hukumomin kiwon lafiya na Japan sun tabbatar da cewa biyu daga cikin wadanda aka dawo da su sun mutu, kamar yadda jami’in ya shaida wa AFP.
Ma’aikatan jirgin sun fito ne daga China da Myanmar, amma ba a san takamaiman ainihin wadanda suka mutu, wadanda aka ceto da kuma wadanda suka bace ba, in ji shi.
Ya kara da cewa “Tasoshinmu za su ci gaba da zama a yankin kuma za su ci gaba da gudanar da bincike cikin dare.”
Jin Tian ya aike da sakon kar ta kwana da yammacin ranar Talata daga wani wuri mai tazarar kilomita 110 yamma da tsibirin Danjo mai nisa da kudu maso yammacin Japan.
Jiragen ruwa masu zaman kansu uku ne a yankin kuma sun taimaka wajen daukar biyar daga cikin ma’aikatan jirgin da ya makale, in ji jami’an tsaron gabar tekun Japan.
Tasoshin ruwa da jiragen sama da yawa daga jami’an tsaron gabar tekun Japan da na soja, da kuma masu tsaron gabar tekun Koriya ta Kudu da wani jirgin ruwa mai zaman kansa, sun shiga aikin laluben wadanda suka bace.
Kyaftin din jirgin ya yi amfani da waya, inda ya shaidawa jami’an tsaron gabar tekun Koriya ta Kudu cewa shi da ma’aikatan jirgin na neman dauki daga jirgin da ya nutse a ruwan.