A ƙalla mutum uku ne suka rasa rayukansu yayin da ambaliyar ruwa ta yi awun gaba da mamaye wasu ƙauyuka a ƙananan hukumomi uku na Shira, Giade da kuma Katagum da suke jihar Bauchi.
Darakta-janar na hukumar samar da agajin gaggawa ta jihar Bauchi (SEMA), Mr. Mas’ud Aliyu ne ya sanar da hakan yayin ziyarar duba irin ɓarna da ambaliyar ruwan ta yi a ƙananan hukumomin.
- Ambaliyar Ruwa Ta Raba Hanyar Bauchi Zuwa Kano
- Gwamnati Ta Amince Da Aikin Titin Sakkwato Zuwa Badagry Da Ayyukan Gina Madatsun Ruwa 63
Ya ce, sun samu rahotonnin da ke cewa, mutum uku ne suka rasu a ƙaramar hukumar Shira yayin da mutane da dama suka rasa muhallai, kayan abinci, amfani gona da kuma yankewar wasu hanyoyi dukka sakamakon mamayar ruwan.
Kazalika, ruwan ya share ƙauyuka da dama inda hakan ya tursasa wa mutanen da ke zaune a yankunan neman inda za su yi gudun hijira.
A ƙaramar hukumar Katagum, shugaban ƙaramar hukumar, Malam Musa Azare ya ce wata ƙauye mai suna Sabon Gari da ke cikin Azare gabaki ɗaya ambaliyar ruwan ya share garin kaf.
Ya ce babu wani gida a ƙauyen da ɓarnar bai shafa ba.
“Mun samu nasarar kwashe mutanen da ke zaune a ƙauyen zuwa wuraren gwamnati da ke kusa da su bisa taimakon gaggawa da gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya samar.
“Abun farin ciki ne mu a Katagum babu asarar rai ko daya da aka samu. Har yanzu muna kan tattara irin ɓarna na ƙadarori da aka samu sakamakon ambaliyar.”
Ya gode wa Gwamna Bala Mohammed bisa aiko fa buhunan kayan abinci 900 dabam dabam domin rabar wa jama’a a matsayin agajin gaggawa. Kayan Abincin sun hada da buhun shinkafa 300, dawa 300, masara 300 da kuma katifu guda 250 da kayan rufuwa.
“Bugu da ƙari, ina miƙa godiyar mu wa mai martaba sarkin Katagum Alhaji Dr. Umar Farouk II, OON, bisa tallafin Naira miliyan biyu da ya bayar ga waɗanda abun ya shafa. Yayin da mu kuma a matakin ƙaramar hukuma mika bayar da gudunmawar miliyan daya ga waɗanda ambaliyar ta shafa.”
A lokacin da yake miƙa kayan abincin da jajanta wa jama’an da ambaliyar ta shafa, sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Muhammad Kashim ya ce sun zo ne domin nuna alhini da kuma taimaka wa waɗanda abun ya shafa musamman a irin wannan halin da suke ciki.
Ya nemi su miƙa lamarin ga Allah kana suke bin shawarorin hukumomi na daina gine-gine a kan magudan ruwa.