Yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza na cikin hatsari yayin da hare-haren sama na Isra’ila suka kashe aƙalla mutum 330 a birnin Falasɗinawa, tare da yiwuwar samun ƙarin mutane da ke maƙale a ƙarƙashin gine-ginen da suka rushe, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Gaza.
Isra’ila ta ƙaƙaba wa Gaza takunkumi tare da umartar wasu yankuna su fice daga gidajensu, wanda ƙungiyar Hamas ta soki hakan, tana mai cewa hakan wani yunƙuri ne na kawo ƙarshen yarjejeniyar zaman lafiyar.
- EFCC Ta Ƙwato Naira Biliyan 365.4 A Shekarar 2024
- Trump Zai Tattauna Da Putin Kan Kawo Ƙarshen Yaƙin Ukraine
Ƙungiyar Falasɗinawa ta Islamic Jihad ita ma ta zargi Isra’ila da karya yarjejeniyar da aka ƙulla tun ranar 19 ga watan Janairu.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce an ƙaddamar da hare-haren ne saboda gazawar tattaunawar tsawaita zaman lafiya.
Ya bayyana su a matsayin “gagarumin farmaki” a kan Hamas, inda ya yi alƙawarin ƙara kai wasu hare-haren.
Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce, “A daren yau mun koma yaƙi a Gaza.”
Hamas ta zargi Isra’ila da karya yarjejeniyar tsawon kusan wata biyu, tana mai cewa hakan na barazana ga lafiyar fursunonin da ke tsare a Gaza.
Amma Isra’ila ta ce Hamas ce ke ƙin sakin fursunonin tare da bijirewa yarjejeniyar sulhu.
A lokacin yarjejeniyar, an yi musayar wasu fursunonin Isra’ila da Falsɗinawa da ke tsare a gidajen yarin Isra’ila.
Sai dai har yanzu kimanin mutum 59 daga cikin fursunonin Isra’ila suna hannun Hamas, kuma ana zargin rabinsu sun mutu.
Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta amince da harin da Isra’ila ta sake kai wa Gaza, inda ƙasashen biyu suka sha alwashin yaƙar Hamas, ‘yan tawayen Houthi na Yemen, da sauran ƙungiyoyin da suka ɗauki makamai.
Kakakin fadar White House, Karoline Leavitt, ta yi gargaɗin cewa, “Hamas da Houthi za su fuskanci sakamako mai tsanani. Duniya za ta girgiza.”
A cewar Ma’aikatar Lafiya ta Gaza, aƙalla Falasɗinawa 48,577 ne suka mutu, yayin da Ofishin Yaɗa Labarai na Gaza ya ce adadin ya haura 61,700, ciki har da waɗanda ke birne a ƙarƙashin gine-ginen da aka rushe.
Yaƙin ya fara ne bayan harin da Hamas ta kai kudancin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023, wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Isra’ilawa 1,139 tare da tsare da sama da mutum 200.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp