Akalla mutum 38 ne suka rigamu gidan gaskiya yayin da wasu kuma su sama da 40 suke kwance a asibiti biyo bayan wani mummunar hatsarin mota da ya rutsa da su a garin Potiskum da ke jihar Yobe a ranar Laraba.
Wakilinmu ya labarto cewa hatsarin ya faru ne a kan hanyar Nangere zuwa Potiskum da ke jihar.
- Xi Ya Gana Da Mataimakin Shugaban Tarayyar Najeriya
- Xi Ya Gana Da Mataimakin Shugaban Tarayyar Najeriya
LEADERSHIP ta gano cewa wata motar tirela ce da ta kwaso shanu daga kauyen Buduwa da ke karamar hukumar Jakusko ce ta yi taho mu kara da wata babbar motar.
“Matukin tirelan yana tsula gudun wuce kima kuma ya rasa iya shawo kan motar nan take ya bugi wata babbar mota da ke kira da Canter Model, inda ya murkushe mutane sama da 20 da jikkata wasu sama da 40,” a cewar ganau.
Wata majiya ta ce, tirelar ta kuma murkushe wadanda suka fado daga cikin daya babbar motar da ya buga.
Zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa ko tabbaci da hukumar kiyaye aukuwar hadura (FRSC) ko sauran hukumomin tsaro a jihar suka fitar dangane da wannan mummunar hatsarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp