Mutane shida sun kone kurmus sannan wasu hudu sun samu raunuka a lokacin da wasu da ake zargin ‘yan ta’addar Boko Haram suka kai hari a yammacin ranar Litinin a garin Gajiram da ke Karamar Hukumar Nganzai a Jihar Borno.
Wasu majiyoyi sun tabbatar wa LEADERSHIP harin a ranar Talata a Maiduguri.
- Kotu Ta Umarci Gwamnatin Tarayya Ta Biya Emefiele N100m Kan Tsare Shi Ba Bisa Ka’ida Ba.
- Gwamnatin Kano Ta Amince Da Kashe Fiye Da Naira Biliyan 1 Domin Biyan Alawus Ga Jami’o’in Jihar
Sun ce lamarin ya faru ne bayan sallar magariba a wata unguwa da ke kusa da wata kasuwa a yankin Gajiram.
Majiyar ta ce, “An kashe mutane shida a jiya bayan sallar magriba a Gajiram, an kuma raunata wasu mutane hudu.
Dakarun soji da kuma rundunar ‘yansandan Jihar Borno ba su fitar da wata sanarwa dangane da faruwar lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp