Akalla mutune takwas ne rahotonni suka ce an kashe a wani sabon rikicin da ya barke tsakanin ‘yan kungiyar asiri a wasu sassan birnin Benin da ke jihar Edo.
Rikicin ya auku ne a yankunan Ugbowo -Uselu, Irhirhi, Ogunmwenhi da kuma Egor, inda a ranar Laraba aka kashe biyar da jikkata mutum guda a rikicin.
Rahotonnin sun kuma ce wasu mutum uku ne aka kashe a safiyar ranar Alhamis a karamar hukumar Egor, inda aka samu adadin mutum takwas duka da aka kashe cikin kwana guda.
Ya zuwa lokacin da wakilin LEADERSHIP ke hada rahoton nan, ba a samu cikakken dalilin da ya janyo barkewar rikici a tsakanin ‘yan kungiyar asirin ba.
Duk kokarin jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar Edo, Chidi Nwabuzor, kan wannan batun abin ya ci tura.