Mutum mutumin inji mai suffar bil’adama kirar kasar Sin, ya kafa matsayin bajimta na “Guinness World Record”, bayan ya yi tattaki na kilomita 106 tsakanin biranen gabashin kasar Sin ba tare da na’urarsa ta mutu ba.
Kamfanin Agibot na birnin Shanghai ne ya kera mutum mutumin inji mai aiki da manhajar Android ta A2, wanda aka dora masa daga birnin Suzhou a daren 10 ga watan nan na Nuwamba, ya kuma isa bakin kogin Huangpu dake birnin Shanghai da sanyin safiyar ranar 13 ga wannan wata.
Har ila yau, mutum mutumin injin yana aiki ne da batiri mai inganci na kamfanin Agibot, ya kuma yi aiki na tsawon dukkanin tafiyarsa, inda a hukumance ya shafe nisan kilomita 106.286, kamar yadda aka tabbatar da hakan a jiya Alhamis. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














