Yusuf Shuaibu" />

Mutum Takwas Sun Mutu A Hadarin Mota A Ogun

An tabbatar da mutuwar mutum takwas ciki har da budurwa, yayin da uwa da danta suka samu mummunar raunika. Hatsarin ya rutsa da wata mota da kuma tirela a garin Ewekoro kan babban hayar Legas zuwa Abeokuta.
Majiyarmu ta ruwaito mana cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 12.50 na dare, lokacin da direban mota kirar ‘Toyota Corolla’ mai fantin kore, mai lamba kamar haka AKD 649 FP, ta kwace masa sannan ta je ta bugi tirelan wacce take tsaye. Nan take mutum bakwai wadanda ake cikin motar suka mutu, inda suka hada da maza hudu mata uku, yayin da budurwan ta mutu a asibiti sakamakon raunin da ta samu a wannan hatsari.
Kakakin hukumar kula da hanya ta Jihar Ogun Babatunde Akinbiyi, wanda ya daura alkakkin hatsarin ga mummunar gudu, ya bayyana cewa, an gano cewa direban yana cikin maye ne. Ya kara da cewa, an ijiye gawarwakin mamatan a dakin ijiye gawarwaki da ke babban asibitin Ifo ta Jihar Ogun. Akinbiyi ya kuma ce, an kai mace mai juna biyu wacce ta samu rauni zuwa asibitin tarayya da ke Idi-Aba cikin garin Abeokuta domin yin jinya.
Akinbiyi ya ce, “Mun samu labarin cewa motar kirar ‘Toyota Corolla’ tana kan hanyar tan a zuwa Abeokuta ne a kan tsohon babban hanyar Legas zuwa Abeokuta lokacin da hatsarin ya auku. “Direban yana cikin maye ne lokacin da motar ta kwace masa sannan kuma yana mummunar gudu sa’ilin day a bugi wannan tirela wanda aka ijiye a gefen hanya, nan take mutum bakwai suka mutu wanda suka hada da maza hudu mata guda uku da ke cikin motar.
“A cikin wadanda suka tsira daga wannan hatsari har da wata mata mai juna biyu, inda a yanzu haka take yin jinya a asibitin tarayya da ke Idi-Aba cikin garin Abeokuta, yiyin da aka tabbatar da mutuwar wata budurwa wanda ta samu rauri a tsarin. “Bireban tilelan baya cikin motar lokacin da hatsarin ya auku, daga baya ya bayyana kansa, inda aka cafke shi aka tafi da shi ofishin ‘yan sanda da ke Ewekoro tare da motar da hatsarin ya rutsa da ita.”

Exit mobile version