Tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna, Muktar Lawal Baloni, ya ajiye mukaminsa tare da ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki nan take.
A cikin wasiƙar murabus da ya aika wa shugaban jam’iyyar APC na mazaɓarsa Kabala, Baloni wanda ya kasance abokin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa abin takaici ne ganin yadda jam’iyyar ta kauce daga manufofin da aka kafa ta a kai.
- ‘Yansanda Sun Hana Gudanar Da Taron Tunawa Da Ranar Haihuwar Obi A Kaduna
- Na Yi Rashin Jagora, Buhari Ne Ya Ƙarfafa Min Guiwa Na Yi Takarar Gwamna A Kaduna — El-Rufai
Ya ce, “Ina rubuto wannan wasika ne domin sanar da murabus ɗina daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), sakamakon banbancin ra’ayin siyasa da kuma manufofin jam’iyyar da nake ganin ba su daidaita da nawa ba a halin yanzu.”
Baloni ya ci gaba da cewa, “Lokacin da na yi a jam’iyyar APC, daga zama ɗaya daga cikin matasan mambobinta na farko, zuwa zama mataimakin shugaban ƙaramar hukuma da daga bisani shugaban ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa, mun shaida yadda mutane suka rungumi jam’iyyar fiye da yadda aka taɓa gani a baya.”
Ya kuma ce, “Wannan ya faru ne saboda jam’iyyar a wancan lokacin ta kasance wani dandali da ke nufin cikar burin talakan Nijeriya ta hanya mai inganci da gaskiya. Abin baƙin ciki ne ganin yadda APC ta dusashe daga asalin aƙidunta kuma siyasar ta ta taɓarɓare. Saboda haka na yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar, domin neman wata jam’iyya da ta dace da aƙidarmu wadda za mu ci gaba da gwagwarmaya don kyautatawa al’umma.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp